• English
  • Business News
Tuesday, October 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wang Yi: Amurka Ba Ta Da Alfarma Ko Gatan Kin Biyayya Ga Dokokin Kasa Da Kasa

by CGTN Hausa
2 years ago
Wang yi

Jiya Alhamis, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da ’yan jaridu tare da takwararsa ta kasar Indonesia Retno Marsudi a birnin Jakarta, fadar mulkin kasar Indonesia. 

A yayin taron, an ce a halin yanzu, gamayyar kasa da kasa na yin kira da a gaggauta tsagaita bude wuta a yankin Gaza, yayin da ake kira ga kwamitin sulhu na MDD da ya ba da gudummawarsa kan wannan aiki. Game da tambayar ko mene ne matsayin kasar Sin kan wannan batu? Wang Yi ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, rikicin yankin Gaza ya tsawaita zuwa rabin shekara, wanda ya haddasa mummunar barazanar jin kai da ba a taba ganin irin ta ba cikin karni na 21.

  • Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Neman Zama Madaukakiya Tare Da Sake Waiwayar Dokokin Kasa Da Kasa
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Ya Gana Da Takwararsa Ta Afirka Ta Tsakiya

Ya ce kwamitin sulhun MDD ya amsa kiran gamayyar kasa da kasa, kuma yana ci gaba da binciken daftarin tsagaita bude wuta a yankin Gaza, amma, sau da yawa, kasar Amurka ita kanta kadai ta yi ta watsi da daftarori masu nasaba da hakan.

Kwanan baya, a karo na farko, kwamitin sulhun MDD ya zartas da kuduri mai lamba 2728, inda aka yi kira da a tsagaita bude wuta a yankin Gaza, amma kasar Amurka ta ce daftarin ba shi da ikon hana ko wane bangare daukar mataki. Lamarin da ya bata ran kasashen duniya, ya kuma bayyana yadda kasar Amurka take son yi wa kasashen duniya mulkin kashin kai. Kaza lika hakan na nuna cewa, kasar Amurka tana bin manufar idan tana so, za ta bi dokokin kasa da kasa, amma idan ba ta so, shi ke nan, za ta yi kyamar dokokin.

Wang Yi ya kara da cewa, kasar Amurka, ba ta da alfarma ko gatan kin biyayya ga dokokin kasa da kasa. Don haka ake fatan Amurkan za ta daidaita tsohon ra’ayinta, tare da nuna goyon baya ga kuduri mai lamba 2728 a matsayin mambar MDD, domin yin hadin gwiwa da sauran kasashen duniya wajen cimma burin tsagaita bude wuta a yankin Gaza.

LABARAI MASU NASABA

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

(Mai Fassarawa: Maryam Yang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka
Daga Birnin Sin

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

October 20, 2025
Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar
Daga Birnin Sin

Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

October 20, 2025
Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

October 20, 2025
Next Post
Shekara 10 Da Sace ‘Yan Matan Chibok: Gidauniya Ta Bayyana Abubuwan Alhini

Shekara 10 Da Sace ‘Yan Matan Chibok: Gidauniya Ta Bayyana Abubuwan Alhini

LABARAI MASU NASABA

An Ɗage Shari’ar Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Zuwa 19 Ga Watan Nuwamba

An Ɗage Shari’ar Shugabannin Ƙungiyar Ansaru Zuwa 19 Ga Watan Nuwamba

October 21, 2025
Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Kasar Sin Na Saurin Bunkasa

October 21, 2025
Mutane 3,433 Sun Rasu a Hatsarin Mota 6,858 Cikin Wata 9 A Nijeriya – FRSC

Mutane 3,433 Sun Rasu a Hatsarin Mota 6,858 Cikin Wata 9 A Nijeriya – FRSC

October 21, 2025
NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Don Biyan Buƙatun ASUU Da Sauran Ƙungiyoyi 

NLC Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Don Biyan Buƙatun ASUU Da Sauran Ƙungiyoyi 

October 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

’Yansanda Sun Kama Ɗan Fashi Sanye Da Kayan NYSC A Enugu

October 21, 2025
Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

October 21, 2025
Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

October 20, 2025
An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

October 20, 2025
Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

October 20, 2025
Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

October 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.