Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a yau Talata cewa, babban sakamakon tattaunawar sulhu tsakanin bangarorin Falasdinawa da aka gudanar a birnin Beijing, shi ne an tabbatar da cewa, kungiyar ‘yantar da Falasdinu Wato PLO ita ce kadai halaltacciyar wakiliyar al’ummar Falasdinu.
Wang, wanda kuma mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin koli na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana hakan ne a yayin bikin rufe tattaunawar sulhu tsakanin bangarorin Falasdinawa. Ya kuma shaida rattaba hannu kan sanarwar kawo karshen rarrabuwar kawuna da karfafa hadin kai da bangarorin Falasdinawa 14 suka yi. (Mai fassara: Yahaya)