Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana jiya Jumma’a cewa, kasarsa tana goyon bayan zaman lafiya, da adalci, da martaba dokokin kasa da kasa, da burin bai daya na mafi yawan kasashe, da kuma tunanin dan Adam kan batun Palasdinu.
Wang ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai, bayan kammala taron tattaunawa kan manyan tsare-tsare karo na 12 tsakanin Sin da EU tare da babban wakilin kungiyar Tarayyar Turai mai kula da harkokin ketare da tsaro, Josep Borrell.
- CMG Ya Kaddamar Da Bikin Baje Kolin “Hanyar Samun Wayewar Kai” A London
- Xi Ya Yi Kira Ga Jiangxi Da Ya Rubuta Nasa Babin A Kokarin Zamanantar Da Kasar Sin
A game da halin da ake ciki yanzu, Wang ya ce abu mai muhimmanci shi ne, cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta, da hanzarta dakatar da rikici, da kiyaye dokokin jin kai na kasa da kasa, da tabbatar da cikakken tsaron fararen hula.
Wang ya bayyana cewa, aiwatar da shirin kafa kasashe biyu ne kadai zai samar da zaman lafiya na zahiri a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma tabbatar da zaman lafiya mai dorewa ga Isra’ila. Kana hanya mafi dacewa ta ciyar da shawarwarin kafa kasashen biyu, ita ce a maido da shawarwarin zaman lafiya cikin sauri, kuma ya kamata dukkan nau’o’in hanyoyin inganta zaman lafiya su taka rawar gani.
Da yake jawabi ga kwamitin sulhu a yayin shawarwarin gaggawa da ta kira jiya Jumma’a, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya bukaci da a hanzarta daukar matakan da suka dace don tabbatar da tsagaita bude wuta tsakanin Falasdinu da Isra’ila.(Ibrahim)