A ranar 19 ga watan nan, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kana ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya aike da sakon taya murna ga Semaya K. Kumba bisa nada shi a matsayin sabon ministan harkokin waje da hadin gwiwar kasa da kasa na Jamhuriyar Sudan ta Kudu.
Wang Yi ya bayyana cewa, a yayin taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka yi a birnin Beijing a watan Satumban bara, shugaba Xi Jinping ya yi wata ganawa mai alfanu da shugaba Salva Kiir Mayardit, inda ya nuna alkiblar raya dangantakar da ke tsakanin Sin da Sudan ta Kudu.
- Tawagar Gwamnati Ta Kai Ziyara Filato, Ta Sha Alwashin Kawo Karshen Kashe-kashe A Jihar
- KOFIN DUNIYA: Za A Kara Yawan Kasashen Da Suke Bugawa Zuwa 64 A Shekarar 2030
Sabon ministan, Monday Semaya K. Kumba ya dade yana aiki a kasar Sin, inda ya nuna namijin kokari wajen karfafa mu’amala da hadin gwiwa a fannoni daban-daban a tsakanin kasashen biyu.
Wang Yi ya ce, yana son yin aiki tare da Monday Semaya, domin aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da karfafa cudanya da hadin gwiwa a tsakanin sassan biyu, da daukaka zumuncin kawancen Sin da Sudan ta Kudu a bisa manyan tsare-tsare. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp