Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya gana a yau Juma’a da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio a Kuala Lumpur na Malaysia, inda suka yi musayar ra’ayi kan danganatkar Sin da Amurka da batutuwan dake jan hankalin kasashensu.
Wang Yi ya yi cikakken bayani kan matsayar Sin game da raya dangantakarta da Amurka, yana mai nanata bukatar bangarorin biyu su aiwatar da muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen suka cimma zuwa manufofi da ayyuka na hakika. Ya ce fatan ita ce Amurka ta kalli Sin da ra’ayi na sanin ya kamata da tsara manufar hulda da Sin bisa burin zaman lafiya da hadin gwiwar moriyar juna da tafiyar da dangantakarta da Sin bisa matsayi na daidaito da girmamawa da moriyar juna, tare da hada hannu da Sin wajen lalubo hanya mai dacewa da za su yi mu’amala ta fahimtar juna a sabon zamani.
Bangarorin biyu sun amince cewa, ganawar ta su ta yi ma’ana, kuma za su karfafa hanyoyin diplomasiyya na tuntubar juna da tattaunawa a dukkan matakai da bangarori, da ba sassan diplomasiyya masu kula da raya dangantakar kasashen biyu damar taka rawar da ta kamata da lalubo bangarorin fadada hadin gwiwarsu yayin da suke hakuri da bambance-bambancen dake tsakaninsu. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp