A yau Lahadi ne mamban hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya zanta da takwaransa na Afirka ta kudu Ronald Lamola, da ta kasar Senegal Yassine Fall, wadanda suka iso kasar Sin gabanin taron FOCAC na bana da za a bude nan da ‘yan kwanaki.
Yayin zantawarsa da mista Lamola, jami’an biyu sun nazarci sakamakon hadin gwiwar Sin da Afirka ta kudu a fannoni da dama, sun kuma bayyana aniyarsu ta fadada hadin gwiwa a bangarori kamar na raya tattalin arziki, da cinikayyar zuba jari, da bunkasa ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da nufin samar da karin gajiya ga al’ummun kasashen biyu. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp