• English
  • Business News
Monday, October 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wang Yi Ya Tattauna Da Takwarorinsa Na Masar Da Jordan Game Da Yanayin Gabas Ta Tsakiya

by Sulaiman and CGTN Hausa
1 year ago
Yi

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya ce, Sin na adawa tare da yin tir da kisan shugaban kungiyar Hamas Ismail Haniyeh a Iran, yana mai bayyana kisan a matsayin abun da ya kara tsananta yanayin da yankin Gabas ta Tsakiya ke ciki, da keta ka’idojin MDD da iko da mutuncin kasar Iran, har ma da yin cikas ga kokarin ingiza zaman lafiya da dakatar da tsagaita bude wuta a zirin Gaza. 

Wang Yi ya bayyana haka ne jiya Talata, yayin tattaunawa da takwaransa na Masar Badr Abdelatty, da na Jordan Ayman Safadi ta wayar tarho, don gane da yanayin da ake ciki a yanyin Gabas ta Tsakiya.

  • Gwamnatin Zamfara Ta Ƙaryata Ware Biliyan 19 Don Sanya Wa Lawal Kayan Girki
  • Tinubu Ya Binciki Kuɗaɗen Da Yake Bai Wa Gwamnoni – Sheikh Yakubu Musa

Ministan na Sin ya kara da cewa, kasarsa za ta karfafa hadin kai da kasashen Larabawa, da ma dukkan bangarori domin kaucewa kara ta’azzarar yanayin da ma tabarbarewarsa.

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

A nasa bangare, Badr Abdelatty ya ce Masar na matukar yabawa muhimmiyar rawar da Sin ke takawa wajen ingiza zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya, tare da kokarin da take yi na sulhunta bangarori masu adawa a cikin Palasdinu.

Ya ce, Masar na fatan ci gaba da tuntuba tsakninta da kasar Sin domin kaucewa ta’azzarar yanayin.

Shi ma Ayman Safadi na Jordan cewa ya yi, ya kamata kasa da kasa su dauki mataki nan take domin kaucewa kazamcewar rikicin Gaza, da dakatar da keta dokokin kasa da kasa, da cimma tsagaita bude wuta ba tare da bata lokaci ba, tare da samar da cikakken ‘yancin kan Palasdinu ta hanyar kafa kasashe biyu.

Ya ce kasar Sin ta dauki matsayi na adalci game da rikicin Palasdinu da Isra’ila, kuma a shirye Jordan take ta ci gaba da tuntuba tsakaninta da kasar Sin, kana ta yi ammana Sin za ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta dakatar da bude wuta da kawo karshen yakin. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka
Daga Birnin Sin

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

October 27, 2025
Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani
Daga Birnin Sin

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

October 27, 2025
Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2025
Next Post
‘Yansanda Sun Ja Hankalin Jama’a Kan Su Guji Rikiɗewar Zanga-zanga Zuwa Rikici A Ribas 

'Yansanda Sun Ja Hankalin Jama'a Kan Su Guji Rikiɗewar Zanga-zanga Zuwa Rikici A Ribas 

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

October 27, 2025
Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

October 27, 2025
Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2025
Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa

Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa

October 27, 2025
Yawan Jigilar Kayayyakin Dake Bukatar Kankara a Kasar Sin Ya Zarce Tan Miliyan 117 a Watannin Yuni Da Yuli Da Agusta

Yawan Jigilar Kayayyakin Dake Bukatar Kankara a Kasar Sin Ya Zarce Tan Miliyan 117 a Watannin Yuni Da Yuli Da Agusta

October 27, 2025
Sin Za Ta Yi Tsayin Daka Wajen Kare Tsarin Cinikayya Tsakanin Mabanbantan Sassa

Sin Za Ta Yi Tsayin Daka Wajen Kare Tsarin Cinikayya Tsakanin Mabanbantan Sassa

October 27, 2025
Xi Ya Halarci Nune-Nune A Babban Gidan Adana Kayan Tarihi Na Karni

Xi Ya Halarci Nune-Nune A Babban Gidan Adana Kayan Tarihi Na Karni

October 27, 2025
Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro

October 27, 2025
Mutanen Katsina Sun Koka Kan Dakatar da Aikin Gyaran Hanyar Mararrabar Kankara–Dutsinma–Katsina

Mutanen Katsina Sun Koka Kan Dakatar da Aikin Gyaran Hanyar Mararrabar Kankara–Dutsinma–Katsina

October 27, 2025
Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?

Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?

October 27, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.