• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wang Yi Ya Yi Bayani Game Da Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka

by Sulaiman and CMG Hausa
3 years ago
Wang Yi

Jiya Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Amurka Joe Biden, a tsibitin Bali na kasar Indonesiya. Bayan ganawar ta su, mamban majalisar gudanarwa, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi karin bayani ga kafofin watsa labarai game da ganawar shugabannin biyu.

Wang Yi ya ce, ganawar shugabannin biyu na da muhimmiyar maana, domin wannan shi ne karo na farko da shugaban kasar Sin da na Amurka suka yi ganawa fuska ta fuska cikin shekaru 3 da suka gabata, kuma karo na farko da shugabannin biyu suka gana da juna fuska ta fuska, bayan shugaban kasar Amurka Joe Biden ya kama aiki. Kaza lika, wannan shi ne karo na farko, da shugabannin koli na kasar Sin da na Amurka suka yi muamala, bayan sun kammala muhimman taruka cikin kasashensu.

Game da batun dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, Wang Yi ya ce, a yayin ganawar shugabannin biyu, an tabbatar da cewa, za a magance tabarbarewar dangantaka a tsakanin kasashen biyu, yayin da ake neman wata hanyar da ta dace ta daidaita dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. Kuma, za a tattauna cikin hadin gwiwa, domin fidda manufar daidaita dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Saan nan kuma, an fara yunkurin aiwatar da raayin shugabannin biyu, ta yadda za a daidaita dangantakar dake tsakanin kasashen biyu cikin yanayin zaman karko.
Haka kuma, a yayin ganawar tasu, shugabannin biyu sun mai da hankali kan batun lardin Taiwan na kasar Sin. Wang Yi ya ce, kasar Sin na fatan Amurka za ta aiwatar da matakai masu nasaba da hakan, kamar yadda ta bayyana, da kuma bin manufar kasar Sin kasa daya tak a duniya”, da sanarwar hadin gwiwa guda uku da kasar Sin da Amurka suka kulla, da kaucewa bata yanayin lardin Taiwan.

Dangane da wannan batu, shugaba Biden ya ce, kasar Amurka tana tsayawa tsayin daka kan manufar kasar Sin kasa daya tak a duniya, kuma ba ta goyon bayan ballewar yankin Taiwan daga kasar Sin, kana kasar Amurka ba ta da burin hana bunkasuwar kasar Sin ta hanyar rura wutar batun Taiwan.

LABARAI MASU NASABA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

Dangane da ci gaban da kasashen biyu suka samu a fannin habaka hadin gwiwa bisa fannoni daban daban, Wang Yi ya ce, a yayin ganawar shugabannin biyu, shugaba Xi Jinping ya ce, bai kamata a dakatar da aikin raya dangantaka a tsakanin kasar Sin da kasar Amurka sakamakon bambancinsu ba, kuma ya kamata kasashen biyu su dukufa wajen tsawaita jerin hadin gwiwar dake tsakaninsu.

Bugu da kari, a yayin ganawar tasu, shugaba Xi ya bayyana matsayin kasar Sin kan wasu batutuwan dake janyo hankulan kasar Amurka, da ma sauran kasashen duniya.

Shugabannin biyu, sun kuma yi musayar raayoyi kan batutuwan dake shafar kasar Ukraine, da batun nukiliyar zirin Koriya da dai sauransu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki
Daga Birnin Sin

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025
Next Post
Ganduje Ya Karrama Dan Sandan Da Ya Ki Karbar Cin Hancin Dala $200,000 A Kano

Ganduje Ya Karrama Dan Sandan Da Ya Ki Karbar Cin Hancin Dala $200,000 A Kano

LABARAI MASU NASABA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025
Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI

Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI

October 25, 2025
An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

October 25, 2025

Daɓid Adeyemi

October 25, 2025
Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

October 25, 2025
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.