Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi bitar nasarorin da aka cimma yayin taron kolin kungiyar hadin kai ta Shanghai ko SCO na shekarar nan ta 2025 da ya gudana a birnin Tianjin.
Taron na SCO irin sa mafi girma da aka gudanar tun kafuwar kungiyar a shekarar 2001, ya hallara shugabannin kasashe sama da 20, da jagororin hukumomin kasa da kasa 10.
Wang, wanda kuma memba ne a hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, ya ce an amince da kudurorin bunkasa ayyukan SCO tsakanin shekarun 2026 zuwa 2035, wanda za su saita alkiblar bunkasa kungiyar cikin shekaru 10 masu zuwa.
Yayin taron manema labarai da ya jagoranta tare da babban sakataren kungiyar ta SCO mista Nurlan Yermekbayev, Wang Yi ya ce an fitar da sanarwar taron na bana, mai kunshe da goyon baya ga nasarar da aka cimma, ta kawo karshen yakin duniya na biyu. Kazalika, cikin wata sanarwar ta daban da aka fitar, kungiyar SCO ta bayyana cikakken goyon bayanta ga tsarin cudanyar cinikayya tsakanin mabanbantan sassa.
Har ila yau, a cewar Wang, yayin taron, an kaddamar da sabbin cibiyoyin SCO guda hudu, wadanda aka dorawa alhakin shawo kan barazanar tsaro da sauran kalubale, da aikin dakile laifukan da ake yi tsakanin iyakokin kasashe daban daban, da kyautata tsaron bayanai, da karfafa hadin gwiwa a fannin dakile yaduwar miyagun kwayoyi.
Bugu da kari, kasashe membobin kungiyar sun amince da kafa bankin bunkasa harkokin SCO, wanda a cewar Wang, zai yi matukar bunkasa samar da ababen more rayuwa, da raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummun kasashe membobin kungiyar.
Dadin dadawa, kasar Sin ta sha alwashin kafa sabon dandalin hadin gwiwa, da cibiyoyi masu nasaba da makamashi, da samar da ci gaba marar gurbata yanayi, da tattalin arzikin dijital, da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da ilimi mai zurfi, da na koyar da sana’o’i da fasahohi. An kuma fitar da tsarin ingiza ci gaba mai inganci, wanda ya kunshi sassa irinsu na makamashi, da masana’antun sarrafa hajoji ba tare da gurbata yanayi ba, da tattalin arzikin dijital, da kirkirarriyar basira ko AI da kirkire-kirkiren fasaha. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp