• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wang Yi Ya Yi Cikakken Bayani Kan Matsayar Sin Game Da Yankin Taiwan

by CMG Hausa
3 years ago
Wang Yi

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya kira taron ganawa da manema labarai a yammacin jiya, bayan ya halarci tarukan ministocin harkokin wajen kasashen gabashin Asiya da aka shirya a birnin Phnom Penh, fadar mulkin kasar Cambodia domin kyautata hadin gwiwa a tsakaninsu. 

Yayin taron manema labaran, Wang Yi ya ce, “Shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosy, ta yi watsi da adawar gwamnatin kasar Sin, ta kai ziyara yankin Taiwan, bisa amincewar gwamnatin kasar Amurka”.

  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Sanar Da Matakan Martani Ga Ziyarar Da Pelosi Ta Kai Taiwan

Ya ce a bayyane yake cewa, ziyararta ta keta ‘yancin mulkin kan kasar Sin, kuma ta tsoma baki cikin harkokin gidan kasar, haka kuma ta sabawa alkawarin gwamnatin Amurka, tare kuma da lahanta zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Taiwan.

Don haka, tabbas kasar Sin ta mayar da martani ta hanyar daukan matakai masu karfi da suka dace bisa matsayar adalci.

Kuma ko shakka babu, atisayen soja da rundunar sojojin kasar Sin take yi a fili, ya dace da dokar kasar, da ta kasa da kasa, da kuma ka’idojin kasa da kasa.

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

A cewar Wang Yi, manufar ita ce, yi wa masu tayar da tarzoma kashedi, da kuma hukunta masu neman ‘yancin kan Taiwan.

Haka kuma, za a ci gaba da daukar matakan da suka dace domin kiyaye ‘yancin mulkin kan kasar Sin da yankunan kasar, da murkushe yunkurin Amurka na hana ci gaban kasar Sin bisa fakewa da batun yankin Taiwan, tare kuma da murkushe makarkashiyar mahukuntan yankin Taiwan na neman ‘yancin kai bisa dogaro da goyon bayan Amurka.

Bugu da kari, Wang Yi ya ce kasar Sin na kokarin kare dokar kasa da kasa, da ka’idar huldar dake tsakanin kasa da kasa, musamman ma ka’idar rashin tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe ta MDD, yana mai cewa, “Idan aka yi watsi da ka’idar, manyan kasashe kamar Amurka za su zalunci kananan kasashe kamar yadda suke so, amma ba zai yiyu kasar Sin ta amince da faruwar irin wannan al’amari ba, kuma ya dace kasashen duniya su hada kai domin hana koma bayan wayewar kan bil Adam.” (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki
Daga Birnin Sin

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka
Daga Birnin Sin

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Next Post
Na Koma Sayar Da Dankalin Turawa Ne Sakamakon Yajin Aikin ASUU – Malamar Jami’ar Oyo

Na Koma Sayar Da Dankalin Turawa Ne Sakamakon Yajin Aikin ASUU - Malamar Jami'ar Oyo

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Majalisar Dattawa

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa

November 5, 2025
Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya

November 5, 2025
Gwamna Yusuf

Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu

November 5, 2025
An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

An Rufe Canton Fair Na 138 A Guangzhou

November 5, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.