Yau Asabar, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi wa manema labarai karin haske game da ganawar da ya yi da takwaransa na Amurka, yayin taron ministocin wajen kasashen gabashin Asiya a birnin Kuala Lumpur na kasar Malasiya.
Wang Yi ya ce, a yayin ganawar, kasar Sin ta yi cikakken bayani kan matsayi da ka’idar da ta dauka kan dangantakar dake tsakaninta da Amurka, da share fagen yin mu’amala ta gaba tsakanin tawagogin diflomasiyyar kasashen biyu. Kuma abu na gaba da ya kamata a yi shi ne, karfafa hulda, da kaucewa yin kuskure, da hakuri da bambance-bambance, da kuma fadada hadin gwiwa.
- An Sanya Kaburburan Sarakunan Daular Xixia Ta Kasar Sin Cikin Muhimman Wuraren Tarihi Na UNESCO
- 2027: Shugabannin Hamayya Sun Bazama Neman Goyon Baya A Yankunansu
Dangane da karin harajin da Amurka ta yi kuwa, Wang Yi ya ce, a bayyane yake cewa matakin ya saba wa ka’idojin kungiyar WTO, kuma yana haifar da koma baya ga ci gaban tattalin arzikin duniya.
Wang Yi ya kuma yi wa manema labarai karin haske kan sakamakon taron ministocin wajen kasashen gabashin Asiya na bana, inda ya ce, Sin da kasashen kungiyar ASEAN sun kammala shawarwarin kafa yankin ciniki cikin ‘yanci na China-ASEAN 3.0, tare da cimma matsaya daya kan shirin aiwatar da hadin gwiwa kan dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare na China-ASEAN a cikin shekaru 5 masu zuwa. Haka kuma sun amince da yin kokarin kammala shawarwarin “ka’idjojin aiwatar da ayyuka a tekun kudancin Sin” a shekarar 2026.
Game da batun tekun kudancin kasar Sin, Wang Yi ya jaddada cewa, ya kamata zaman lafiya da kwanciyar hankali da hadin gwiwa su zama babban abin da ya fi daukar hankali a kan batun tekun kudancin kasar Sin.
Har ila yau a wannan rana, Wang Yi ya gana da ministan harkokin wajen Sri Lanka Vijitha Herath a birnin na Kuala Lumpur.
Bugu da kari, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya mai da martani a yau Asabar game da furucin da Philippines ta yi kan sanarwa game da bikin cika shekaru 9 da fitar da hukuncin takkadamar “Philippines v. China”, inda ya bayyana cewa, “hukuncin” ya saba wa ka’idojin dokokin kasa da kasa da kuma yarjejeniyar MDD kan batun teku, kuma ya sabawa ainihin gaskiyar dake tattare da batun tekun kudancin kasar Sin, haka kuma ba shi da wata daraja ko amfani.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp