ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, November 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wang Yi Ya Yi Tsokaci Kan Matsayar Sin A Batun Tekun Kudancin Kasar

by CMG Hausa
3 years ago

LABARAI MASU NASABA

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen dake yankin gabashin Asiya karo na 12 a birnin Phnom Penh, fadar mulkin kasar Kambodia, jiya Juma’a 5 ga wata, inda ya yi tsokaci kan matsayar da kasar Sin ta dauka kan batun da ya shafi tekun kudancin kasar, tare da yin tir da kulawar da Amurka ta nuna.

Wang Yi ya bayyana cewa, matsayar kasar Sin kan tekun kudanci tana bisa doron doka da tarihi, kuma kasar Sin ba ta taba sauya matsayarta ba, wato kasar Sin da kasashe mambobin kungiyar ASEAN, sun daidaita sabanin dake tsakaninsu ta hanyar tattaunawa bisa “sanarwar bangarorin da tekun kudancin ya shafa”.

Ya ce a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, kasar Sin da kasashen ASEAN sun yi kokari tare, domin tabbatar da kwanciyar hankali a tekun, ta yadda za su samu ci gaba tare.

ADVERTISEMENT

Wang Yi ya kara da cewa, a halin da ake ciki yanzu, wadda ke kawo hadari ga kwanciyar hankalin yankin tekun kudanci ita ce Amurka, duk da cewa, ba ta taba nuna rashin amincewa kan matsayar kasar Sin a yankin tekun ba cikin lokaci mai tsawo, amma yanzu ta musunta matsayar kasar Sin ta kowacce fuska, kuma matakin da ta dauka ba shi da dalili ko tushen doka ko kadan, yana mai cewa, idan wata babbar kasa ta sauya manufarta kamar yadda take so bisa bukatun siyasa, shin ina amana da kimarta suke? (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam
Daga Birnin Sin

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

November 11, 2025
Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa
Daga Birnin Sin

Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

November 11, 2025
CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya
Daga Birnin Sin

CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya

November 11, 2025
Next Post
Ma’aikata 2 Sun Shiga Hannu Kan Zargin Sace Tiraktocin Taki 9 A Nasarawa

Ma'aikata 2 Sun Shiga Hannu Kan Zargin Sace Tiraktocin Taki 9 A Nasarawa

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna

Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna

November 12, 2025
Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba

Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba

November 12, 2025
Coas

Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro

November 11, 2025
Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam

November 11, 2025
Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

Bikin CIIE Ya Nuna Yadda Sin Ke Ba Da Jagora Kan Harkokin Bude Kofa

November 11, 2025
Za Mu Ci Gaba Da Tallafa Wa ’Yansanda Domin Inganta Ayyukan Su A Zamfara – Gwamna Lawal

Za Mu Ci Gaba Da Tallafa Wa ’Yansanda Domin Inganta Ayyukan Su A Zamfara – Gwamna Lawal

November 11, 2025
CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya

CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya

November 11, 2025
CMG Ya Gabatar Da Sabbin Manhajoji 10 Da Ya Kirkiro Don Watsa Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Kasar Sin Karo Na 15

CMG Ya Gabatar Da Sabbin Manhajoji 10 Da Ya Kirkiro Don Watsa Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Kasar Sin Karo Na 15

November 11, 2025
‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3 A Nasarawa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3 A Nasarawa

November 11, 2025
Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina

Cikin Wata Ɗaya, ‘Yansanda Sun Kama Mutane 200 Da Ake Zargi Da Laifuka A Katsina

November 11, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.