• Leadership Hausa
Monday, August 8, 2022
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Kotu Da Ɗansanda

Ma’aikata 2 Sun Shiga Hannu Kan Zargin Sace Tiraktocin Taki 9 A Nasarawa

by Khalid Idris Doya
2 days ago
in Kotu Da Ɗansanda
0
Ma’aikata 2 Sun Shiga Hannu Kan Zargin Sace Tiraktocin Taki 9 A Nasarawa
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Akanta da jami’in kula da dakin ajiye kayayyaki na ma’aikatar gona da albarkatun kasa na jihar Nasarawa sun shiga hannun da zarginsu da ake yi na karkatar da tiraktocin guda tara na Takin zamani da aka samar da zimmar raba wa manoma a sassan kananan hukumomin 13 da ke jihar.

Kwamishinan ma’aikatar gona ta jihar Hon. Nuhu Ibrahim-Oshafu, shine ya shaida hakan a lokacin da jami’an ma’aikatar gona na jihar Nasarawa da ma’aikatar bunkasa harkokin gona ta jihar (NADP) suka bayyana a gaban kwamiti domin kare kwazon kasafin kudi na 2022.

  • Wang Yi Ya Yi Tsokaci Kan Matsayar Sin A Batun Tekun Kudancin Kasar
  • Ko Kananan Sana’o’i Na Biya Wa ‘Yan Nijeriya Bukatunsu?

Ibrahim-Oshafu, ya ce, ma’aikatar ta sayo da raba tiraktoci Taki 21 da aka sayo a kan kudi naira miliyan N238 a jihar.

Ya ce a lokacin da ya shiga Ofis domin kama aiki, 12 da rabin tiraktocin takin ne aka mika masa, ya ce amma da suka je dakin ajiye kayayyaki sai suka gano tiraktocin 9 sun yi baton dabo.

Ya ce an cafke Akanta da jami’in kula da dakin ajiye kayayyaki bisa zargi da hannu a bacewar takin kuma tunin aka dakatar da su a yayin da bincike ke cigaba da gudana kan lamarin.

Labarai Masu Nasaba

Kotu Ta Tsare Dan Kasuwa Kan Zargin Daure Matar Aure Na Tsawon Mako 2

Kotu Ta Raba Auren Wanda Ya Auri Jikarsa A Zamfara

Shi kuma Manajan NADP, Mr Emmanuel Allahnana, da ya bayyana a gaban kwamitin ya ce akwai karancin malaman gona da jihar ke fama da shi don haka ya roki a dauki karin ma’aikata domin shawo kan matsalolin da ake fuskanta a fannin harkokin noma domin bunkasa harkokin abinci a jihar.

Da yake maida bayani kan batutuwan da suke akwai, Shugaban kwamitin gona na Majalisar Dokokin Jihar, Mr. Ibrahim Peter-Akwe, ya roki gwamnatin jihar ta ayyana dokar ta baci a bangaren noma, ya kuma gargadi ma’aikatan dangane da karancin Taki da manoma ke samu a jihar.

Ya ce fannin gona na da muhimmanci a jihar don haka da bukatar gwamnati ta dauki matakan shawo kan matsalolin da suke akwai a bangaren gona.

Tags: HukumomiHukunciJami'an TsaroKotuMa'aikata 2TiraktociTsarewaZargi
ShareTweetSendShare
Previous Post

Wang Yi Ya Yi Tsokaci Kan Matsayar Sin A Batun Tekun Kudancin Kasar

Next Post

Kasar Sin Na Gudanar Da Atisayen Soji A Rawayen Teku Da Tekun Bohai

Related

Kotu Ta Raba Auren Wanda Ya Auri Jikarsa A Zamfara
Kotu Da Ɗansanda

Kotu Ta Tsare Dan Kasuwa Kan Zargin Daure Matar Aure Na Tsawon Mako 2

2 days ago
Kotu Ta Raba Auren Wanda Ya Auri Jikarsa A Zamfara
Kotu Da Ɗansanda

Kotu Ta Raba Auren Wanda Ya Auri Jikarsa A Zamfara

3 days ago
An Kama Wani Mutum Yana Jima’i Da Akuya A Ogun
Kotu Da Ɗansanda

An Kama Wani Mutum Yana Jima’i Da Akuya A Ogun

3 days ago
Dubun Wasu Mazambata Da Kakin Soja Ta cika A Legas
Kotu Da Ɗansanda

Dubun Wasu Mazambata Da Kakin Soja Ta cika A Legas

1 week ago
Matar Sufeto Ta Gurfanar Da Kurtun Dan Sanda A Kotu Kan Kashe Mijinta
Kotu Da Ɗansanda

Ta Soka Wa Mijinta Wuka Ya Mutu Saboda Ya Sha Giya

1 week ago
Mutum 25 Ne Suka Bace Cikin Wata 6 A Jihar Abia — ‘Yan Sanda
Kotu Da Ɗansanda

‘Yan Sanda Sun Cafke Wasu Mutane 4 Da Ake Zargi Da Kashe Hadimin Omo-Agege A Delta

1 week ago
Next Post
Kasar Sin Na Gudanar Da Atisayen Soji A Rawayen Teku Da Tekun Bohai

Kasar Sin Na Gudanar Da Atisayen Soji A Rawayen Teku Da Tekun Bohai

LABARAI MASU NASABA

Kungiyar ASUU Ta Bukaci Soke Jarrabawar Jami’ar Jihar Kaduna

Kungiyar ASUU Ta Bukaci Soke Jarrabawar Jami’ar Jihar Kaduna

August 8, 2022
Yawan Musayar Kudaden Da Aka Adana Na Sin A Karshen Watan Yuli Ya Kai Dalar Tiriliyan 3.1041

Yawan Musayar Kudaden Da Aka Adana Na Sin A Karshen Watan Yuli Ya Kai Dalar Tiriliyan 3.1041

August 8, 2022
Wani Dalibin Sakandire Ya Hada Mutum-Mutumi Mai Motsi A Kano

Wani Dalibin Sakandire Ya Hada Mutum-Mutumi Mai Motsi A Kano

August 8, 2022
Lardin Hunan Na Kasar Sin Da Kasashen Afrika Na Gwajin Biyan Kudin Cinikayya Da Takardun Kudadensu

Lardin Hunan Na Kasar Sin Da Kasashen Afrika Na Gwajin Biyan Kudin Cinikayya Da Takardun Kudadensu

August 8, 2022
Kowa Ya San Ainihin Makasudin Pelosi Kan Hujjarta Ta “Demokuradiyya”

Kowa Ya San Ainihin Makasudin Pelosi Kan Hujjarta Ta “Demokuradiyya”

August 8, 2022
Tsohon Shugaban Hukumar Binciken Sararin Samaniya Ta Kasa NARSDA, Ya Rasu

Tsohon Shugaban Hukumar Binciken Sararin Samaniya Ta Kasa NARSDA, Ya Rasu

August 8, 2022
Wang Yi: Bangarori 3 Na Kuskuren Da Amurka Ta Yi Kan Batun Taiwan

Wang Yi: Bangarori 3 Na Kuskuren Da Amurka Ta Yi Kan Batun Taiwan

August 8, 2022
“El-Rufai Zai Koma PDP Kafin 2023”

“El-Rufai Zai Koma PDP Kafin 2023”

August 8, 2022
Ziyarar Nancy Pelosi Zuwa Taiwan Takala Ce Mai Muguwar Manufa

Ziyarar Nancy Pelosi Zuwa Taiwan Takala Ce Mai Muguwar Manufa

August 8, 2022
An Saki Tsofaffin Gwamnoni, Dariye Da Nyame Daga Gidan Yarin Kuje

An Saki Tsofaffin Gwamnoni, Dariye Da Nyame Daga Gidan Yarin Kuje

August 8, 2022
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.