Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron majalisar shugabannin kasashen mambobin kungiyar hadin gwiwar Shanghai karo na 22 a birnin Samarkand, tare da kai ziyarar aiki a kasashen Kazakhstan da Uzbekistan bisa gayyatar da aka yi masa, tsakanin ranakun 14 zuwa 16 ga wannan wata.
Mamban majalisar gudanarwar kasar kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya yi bayani kan ziyarar shugaban ga manema labarai.
Yana mai cewa, ziyarar da shugaba Xi Jinping ya yi, ita ce ziyara ta farko da ya kai zuwa ketare, tun bayan barkewar annobar cutar COVID-19, don haka tana da ma’ana ta musamman, ra’ayin jama’ar kasa da kasa na ganin cewa, shugaba Xi ya zabi kasar dake tsakiyar nahiyar Asiya, domin yin ziyararsa ta farko, tun bayan bazuwar cutar, lamarin yana da babbar ma’ana, saboda ziyarar za ta ba da gudummowa ga kasar Sin, yayin da take kokarin dakile yunkurin kasar Amurka na hana ci gabanta, bisa taimakon aminai kasashen mambobin kungiyar hadin gwiwar Shanghai, hakan ya nuna hikima da imani da hangen nesa na shugaba Xi.
Yana mai bayyana cewa, matsayin kasar Sin a duniya da tasirin da take yi a fadin duniya suna karuwa.
Wang Yi ya kara da cewa, yayin ziyararsa ta tsawon sa’o’i 48, shugaba Xi ya halarci ayyukan da aka shirya kusan 30, tare kuma da samun babban sakamako, ana iya cewa, ziyarar Xi ta ciyar da kungiyar hadin gwiwar Shanghai gaba yadda ya kamata, kana ta sa kaimi da ci gaban huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen da abin ya shafa. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)