Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta sanar a yau Asabar cewa, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, zai halarci babban taron MDD karo na 77 da zai gudana daga ranar 18 zuwa 25 ga watan Satumban da muke ciki.
A tsawon wannan lokaci, Wang Yi zai jagoranci taron ministocin “Rukunin aminan shirin raya kasa na duniya”, zai kuma halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen BRICS dake babban zauren MDD da sauran ayyuka, zai kuma gana da babban sakataren MDD, da shugaban babban taron MDD karo na 77, gami da shugabannin tawagogin wasu kasashe. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp