Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, zai halarci taron karawa juna sani game da tsaro na Munich karo na 60, kana zai gudanar da ziyarar aiki a kasashen Sifaniya da Faransa.
Da take tabbatar da hakan cikin wata sanarwa a Alhamis din nan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning, ta ce yayin taron na Munich, Wang Yi zai gabatar da jawabi game da kasar Sin, da matsayarta don gane da muhimman batutuwan da suka shafi duniya bisa taken taron. Daga nan kuma zai ziyarci kasashen Sifaniya da Faransa, kana zai halarci taron tattaunawa tsakanin Sin da Faransa bisa manyan tsare-tsare a birnin Faris, tsakanin ranaikun 16 zuwa 21 ga watan nan na Fabrairu.
- Gwamna Lawal Ya Karɓo Sakamakon Jarabawar WAEC Da Hukumar Ta Riƙe
- Sin Ta Yi Kira Ga Kasashe Masu Ci Gaba Da Su Kara Samar Da Gudummawar Jin Kai Ga Kasashe Masu Tasowa Mabukata
Kaza lika cikin wata sanarwar ta daban, Mao Ning ta ce, a gabar da duniya ke fuskantar sauye-sauye a wannan karni, da sabon lokaci na canji da gargada, Wang zai fayyacewa taron na Munich matsayar Sin game da gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ga daukacin bil Adama, kana zai yayata manufar samar da daidaito, da oda a tsarin duniya mai tasirin sassa daban daban.
A daya bangaren kuma, ziyarar da Wang zai kai Sifaniya, na zuwa ne yayin da alakar Sin da Sifaniya ke shiga shekaru 50 na biyu, kuma a wannan gaba Sin na fatan ziyarar za ta baiwa sassan 2 damar kara zurfafa aiwatar da ra’ayi daya na fahimtar juna da shugabanninsu suka cimma, da karfafa amincewa da juna, da yaukaka abota, da ingiza hadin gwiwa, da inganta cikakkiyar alakar sassan biyu daga dukkanin fannoni.
Bugu da kari, Wang zai zanta da tsagin kasar Faransa, zai kuma yi jagorancin taron tattaunawa na zabon zagaye tsakanin bangaren Sin da Faransa bisa manyan tsare-tsare.
Mao Ning ta kara da cewa, Sin na fatan yin aiki tare da Faransa, wajen kara zurfafa muhimmiyar tattaunawa, da yaukaka amincewa da juna ta fuskar siyasa, da ingiza hadin gwiwa a zahiri, da musaya tsakanin al’ummunsu, da musaya ta fannin al’adu. (Saminu Alhassan)