Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, zai jagoranci taron kolin masu tsara aiwatar da ayyukan da suka biyo bayan taron ministocin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) gobe Alhamis 18 ga watan Agustan da muke ciki.
Mambobin hukumar zartaswar taron kolin kungiyar tarayyar Afirka, da kasashen Senegal, da Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, da Libya, da Angola da wakilan ministocin kasashen Habasha, da Masar da Afirka ta Kudu, wato tsoffin shugabannin Afirka na dandalin FOCAC, da wakilan hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka, za su halarci taron. (Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp