A bisa sakon da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar, daga ranar 18 zuwa 20 ga watan Agusta, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kuma ministan wajen Sin, kana wakilin musamman na bangaren Sin kan batun iyakar kasashen Sin da Indiya, Wang Yi, zai ziyarci kasar Indiya bisa gayyatar kasar, tare da gudanar da taron wakilan musamman kan batun iyakar kasashen biyu karo na 24.(Safiyah Ma)













