Daga ranar 2 zuwa 6 ga watan Yuli, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron majalisar shugabannin kasashen mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO da aka gudanar a birnin Astana, fadar mulkin Kazakhstan, kuma an gayyace shi da ya kai ziyarar aiki a kasashen Kazakhstan da Tajikistan. A karshen ziyarar, mamban ofishin siyasa na kwamitin koli na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya yi wa manema labarai karin bayani kan ziyarar.
Ya ce, ziyarar ta shugaba Xi ta sa kaimi ga bunkasuwar kungiyar SCO don zuwa wani sabon mataki, da wadata sabuwar ma’ana ga al’ummar Sin da Kazakhstan mai makoma bai daya, da sa kaimi ga kafa sabon matsayi na dangantakar dake tsakanin Sin da Tajikistan, da zurfafa dangantakar dake tsakanin kasashe makwabta, da kuma inganta karuwar karfin zaman lafiya na duniya, shi ya sa ziyarar nan ta samu nasara sosai. (Safiyah Ma)