Wasu da ba a san ko su wanene ba sun kai hari gidan yarin Kuje da bama-bamai a daren ranar Talata.
Majiyoyi sun ce ana ci gaba da harbe-harbe da karar fashewar abubuwa a kusa da wurin, wanda ke wani yanki da ake kira Shetuko a karamar hukumar Kuje.
- Sallah: ‘Yan Bindiga Sun Kai Wa Tawagar Shugaba Buhari Hari A Hanyarsa Ta Zuwa Katsina
- Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina Ta Tabbatar da Kashe Jami’inta, ACP Aminu Umar
Har zuwa lokacin da muke hada wannan rahoto, ba a tabbatar da ainihin musabbabin faruwar lamarin ba amma majiyoyin da ke kusa da wurin sun ce suna zaton harin ta’addanci ne.
Da aka tuntubi Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda (AIG), shiyya ta 7 a Abuja, Aliyu Ndatsu, ya shaida wa LEADERSHIP cewa yana zantawa da jama’a a kasa inda ya kuma yi wa wakilinmu karin haske.
Da yuyuwar samun cikakkun bayanai daga baya…
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp