Wani abun fashewa a wani masallaci a birnin Herat a yammacin Afghanistan ya kashe wani babban malamin nan mai goyon bayan Taliban da kuma fararen hula fiye da goma.
- Mayakan Taliban Sun Yi Arangama Da Masu Gadin Iyakar Iran
- Biden Bai Cimma Yunkurinsa Kan Batun Yankin Gabas Ta Tsakiya Ba
Hotunan da aka yi a shafukan sada zumunta a ranar Juma’a sun nuna wasu gawarwaki masu dauke da jini a warwatse a harabar masallacin. Babu wani da ya dauki alhakin kai harin.
Kakakin gwamnan lardin Herat, Hameedullah Motawakel, ya shaida wa manema labarai cewa, mutane 18 ne suka yi shahada a lamarin, yayin da wasu 23 suka jikkata.
Fashewar ta tashi ne a cikin masallacin Guzargah a lokacin ake tsaka da gudanar da sallah.
“[Imam] Mujib Rahman Ansari tare da wasu masu gadinsa da fararen hula an kashe su akan hanyarsu ta zuwa masallaci,” in ji kakakin ‘yan sandan Herat Mahmoud Rasooli. “Daya daga cikin ‘yan kunar bakin waken ya tarwatsa kansa yayin da yake sumbatar hannayensa.”
Kakakin Taliban Zabihullah Mujahid ya ce za a hukunta wadanda suka kai harin bam.
Mujahid ya fada a shafinsa na Twitter cewa “Jarumi kuma jajirtaccen malamin addini na kasar ya yi shahada a wani mummunan hari.”