Gwamnatin jihar Kaduna, ta ce ta samu rahotanni daga jami’an tsaro a jihar cewa a daren ranar Asabar wani bam ya tashi a wata makarantar Islamiyya da ke unguwar Kidandan ta karamar hukumar Giwa a jihar, inda ya kashe wani dalibi daya tare da jikkata wasu mutum 10.
Wata sanarwa da mukaddashin kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya fitar ya tabbatar da rahoto kan mutuwar wani dalibi daya mai suna, Zaidu Usman, yayin da wasu mutum 10 suka jikkata yanzu haka suke karbar kulawar jami’an lafiya a asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika.
- ‘Yan Fashin Daji Sun Kai Wani Sabon Hari Sun Kashe Mutum 6 A Yankin Kudancin Kaduna
- Rashin Tsaro: Gwamnatin Kaduna Za Ta Kafa Asusun Hadaka Don Tsaron Jihar
Aruwan, ya kara da cewa gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya samu rahoton cikin yanayi na bacin rai da damuwa, ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga wadanda abin ya shafa da iyalansu, inda ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu, ya ba wadanda suka ji rauni lafiya.
Gwamnan ya kuma yi kira ga iyaye da shugabannin al’umma da su kara sanya idanu kan ‘ya’yansu da unguwannin su don kaucewa fadawa hadurruka daban-daban.
Aruwan, ya ce gwamnan ya umurci ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida da ta hada kai da hukumomin tsaro domin gudanar da bincike cikin gaggawa kan musabbabin fashewar abun, domin tabbatar da tsaron lafiyar jama’a, da samar da agajin gaggawa da kuma tabbatar da kulawar ga wadanda abin ya shafa.