Rundunar Sojin Nijeriya ta ce, wani Bom samfurin (IED) da mambobin kungiyar IPOB suka dasa ya tarwatse tare da jikkata mutum biyu daga cikinsu.
Daraktan yada labarai na Sojoji, Brig. Gen. Onyema Nwachukwu, ya shaida hakan acikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba a kan hanyar Eke Ututi-Orsu da ke karamar hukumar Orsu a jihar Imo.
Ya ce, “Mun gano cewa, mambobin IPOB sun dasa abun fashewar ne da nufin jikkata sojoji sai kuma kaikayi ya koma kan mashekiya.
“Yan kungiyar sun jima suna dasa wa Sojoji abubuwan fashewa da zimmar illata su, amma hakarsu ba ta cimma ruwa,” .
Kakakin sojan ya bukaci al’ummar kudu Maso Gabas da sukai rahoto ga Sojoji Kan duk wani motsin mambobin IPOB din domin dakile aniyarsu na kawo cikas ga tsaron kasa a kowani lokaci.