Kamfanin hakar ma’adinai na Jiuling Lithium, na kasar Sin, na shirin zuba jarin sama da dala miliyan 200 a domin haƙar lithium a Endo da ke jihar Nasarawa.
A ziyarar da gwamna Abdullahi Sule ya kai, shugaban kamfanin, Mista Xiong Jin, ya jaddada aniyarsu ta gina daya daga cikin manyan masana’antar samar da lithium a jihar. Ya kuma bayyana cewa ma’aikatan da aka dauka aiki a wurin za su sami mafi karancin albashi na N500,000.
- Saurayi Ya Fille Kan Budurwarsa A Nasarawa
- Gwamna Sule Ya Rushe Majalisar Zartarwar Nasarawa, Ya Sauke Sakataren Gwamnati
Gwamna Sule ya bukaci matasa da su rungumi sana’o’in hannu domin cin gajiyar guraben ayyukan yi a fannin hakar ma’adinai.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar hukumomin tarayya na daukar matakan da suka dace domin ganin an samu nasarar aikin.














