Aikin fadada tashar samar da wutar lantarki mai aiki da hasken rana a kasar Zambiya ya fara samar da wutar lantarki a garin Kitwet dake lardin Copperbelt a ranar 15 ga watan. Kamfanin kasar Sin, wato China Hydropower Construction Group ne ya kammala wannan sabon aiki. Shugaban Zambiya Hakainde Hichilema ya halarci bikin kaddamar da aikin.
Hichilema ya bayyana cewa, kara yawan wutar lantarki da ake samarwa bisa karfin hasken rana a gyefen kogin, na kamfanin Copperbelt Energy na Zambiya zuwa 34MW, da nasarar samar da wutar lantarki zuwa ga tsarin turakun tattara wutar lantarki, yana da babbar ma’ana ga kasarsa. Kasar Zambiya ba ta son ci gaba da shan wahalhalu sakamakon rashin wutar lantarki. Sabo da haka, wannan aiki zai taka muhimmiyar rawa ga kokarin cimma wannan buri nan gaba.
Wannan sabon shirin samar da wutar lantarki mai aiki da hasken rana yana yankin garin Kitwet na lardin Copperbelt. Yawan filin da shirin ya mamaye ya kai hekta 31.5. Bisa shirin da aka tsara, bayan wannan sabon shiri ya fara aiki, za a iya samar da wutar lantarki fiye da megawatt miliyan 56 a duk shekara. (Safiyah Ma)