An tsinci gawar wani Matashi rataye a jikin bishiyar Mongoro a garin Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti.
An gano mamacin da suna Tunde Akindunbi da aka wayi gari da ganin gangar jikinsa a safiyar ranar Asabar a yankin Dallimore.
Mutane da dama da su ga gawar tasa sun yi amannar cewa Akindunbi ya rataye kansa da kansa ne. A yayin da wasu kuma suke da ra’ayin cewa yadda aka ga gawar tasa a saman bishiya to ba shi ne ya rataye kansa da kansa ba.
Su na masu cewa, kila wasu ne suka kashe shi amma suke son binne duk wata kafa ta bibiya da binciken da zai kai a ganosu.
Wata majiya daga yankin ta ce, akwai yiyuwar cewa an kashe matashin ne tun a daren ranar Juma’a.
Wani ma kuma ya ce, mamacin ya yanke hukunci kawo karshen rayuwarsa ne sakamakon rashin jituwa da suka samu a kwanakin baya da budurwarsa.
A takaice dai har zuwa yanzu babu takamaimai dalilin da ya janyo mutuwar matashin har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Lokacin da aka tuntubi Kakakin hukumar ‘yansandan jihar Ekiti, DSP Sunday Abutu, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce, tunin ‘yansanda suka kaddamar da bincike kan lamarin.
Abutu ya kara da cewa zuwa yanzu an gayyaci mutane biyu domin su amsa tambayoyi dangane da abun da ya faru.