• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wani Rahoton Aiki Mai Burgewa

by Sulaiman
3 years ago
JKS

Rahoton da babban sakataren jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) Xi Jinping ya gabatar a jiya Lahadi, a yayin bude babban taron wakilan JKS karo na 20 yana da burgewa sosai, saboda cike yake da bayanai masu nasaba da tunanin dora muhimmanci kan moriyar jama’a.

A cikin rahoton, yayin da ake bayyana nasarorin da jam’iyyar ta cimma a shekarun baya, an fi dora mihimmanci kan yadda ta kare rayuka da lafiyar al’umma daga cutar COVID-19, da kawar da talauci a kasar Sin, da kafa tsarin ilimi, da aikin lafiya, da ba da tabbaci ga ingancin zaman rayuwar jama’a mafi girma a duniya.

  • Yadda Kauyen Xiaoheifa Ke Kokarin Rungumar Kyakkyawar Makomarsa A Kasar Sin

Kana a bangaren ayyukan da za a yi a nan gaba, an jaddada bukatar daidaita matsalolin da suka fi damun jama’a, da samar da isassun damammakin raya kai.

Ban da bayanan rahoton, wasu wakilan JKS mahalartar taron, su ma sun shaidawa manema labaru, yadda tunanin dora muhimmanci kan moriyar jama’a yake yin amfani a kasar.

Zulyati Simayi, wakiliyar JKS ce da ta zo daga jihar Xinjiang ta kasar Sin. Ta yi bayani kan labarin wata yarinya ‘yar Uygur: Wannan yarinya da aka haifa a gundumar Wensu ta garin Aksu, bayan da ta kammala karatun sakandare, ta shiga makarantar koyar da ilimin sana’a, inda ta koyi fasahar hannu ta dinki domin kawata tufafi.

LABARAI MASU NASABA

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Daga baya ta fara aiki a ma’aikatar samar da tufafi don neman inganta fasaharta ta dinki. Zuwa yanzu, bisa tallafin gwamnati, ta kafa wata ma’aikatar dinkin tufafi ta kanta, inda ta samar da dimbin guraben aikin yi ga matasa.

A nata bangare, Jiang Lijuan, matar dake rike da mukamin dagacin kauyen Xiajiang dake lardin Zhejiang na kasar Sin, ta yi bayani kan yadda mutanen kauyenta suke ta cimma burin samun karin kudin shiga.

Ta ce a shekarar 2021, kudin shigar duk mutum daya a tsawon shekara a kauyenta ya kai dalar Amurka 6,522, jimillar da ta ninka ta shekarar 2003 har sau 14. Wannan lamari ya nuna yadda jam’iyyar mai rike da ragamar mulki a kasar Sin, wato JKS, take kokarin sanya ci gaban tattalin arzikin kasar a matsayin abun da zai amfani kowanne mutum na kasar.

Ko shakka babu, yadda ake mai da hankali kan moriyar jama’a, ya sa kasar ta Sin ta dora muhimmanci kan makomar bai daya ta daukacin bil Adama, ta fuskar manufar huldar kasa da kasa ta kasar. Wannan tunani shi ma yana cikin rahoton JKS dake kan karagar mulki a kasar.

A cewar Lin Zhanxi, wakilin JKS, kuma kwararre a fannin nazarin fasahohin aikin gona, shi da tawagarsa na kokarin yayata fasahar noman laimar kwado a duniya, bisa goyon bayan da gwamnatin kasar Sin ta ba su.

Dalilin da ya sa ake yin haka, shi ne wannan fasaha ta taka muhimmiyar rawa, a kokarin kasar Sin na fid da manoma daga kangin talauci. Yanzu haka an horar da ma’aikata fiye da 12,000 a kasashe masu tasowa da dama, wadanda suka yada fasahar zuwa wasu kasashe da yankuna 106.

Ta wadannan misalai, ana iya ganin yadda JKS take kokarin kare moriyar jama’ar kasar Sin, gami da ta dukkan dan Adam, bisa babbar manufarta ta kokarin bautawa jama’a.

Wannan manufar ita ce dalilin da ya sa ta samu damar rike ragamar mulki a kasar Sin har tsawon shekaru 73, kuma take ci gaba da samun goyon baya daga al’ummar kasar Sin. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26
Daga Birnin Sin

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Next Post
Jami’ar Bayero Ta Sanar Da Ranar Bude Makaranta Don Ci Gaba Da Karatu

Jami'ar Bayero Ta Sanar Da Ranar Bude Makaranta Don Ci Gaba Da Karatu

LABARAI MASU NASABA

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

October 9, 2025
SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.