Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna da ke ta kama wani shahararren dan bindiga da ke addabar mutanen jihar Bilyaminu Sa’idu a karamar hukumar Zariya.
Kakakin rundunar, DSP Mohammed Jalige, ya ce ‘yan sandan da ke aiki a yankin Tudun Wada Zariya ne suka kama dan bindigar yayin da suke samame a Kwarkwaron Manu yankin Basawa inda suka tare wasu mutum biyu a kan babur da ba shi da lamba.
Ya kara da cewa mutanen suna dauke da wasu jakunkuna da ake zargin an boye bindigogi.
Bayan an tare su ne, sai daya daga cikinsu ya yi yunkurin tserewa lamarin da ya sa aka kama shi.
An gano bindigogi kirar AK47, da harsasai dari uku da arba’in da wayoyin salula goma da kuma magunguna a cikin jakar. BBC Hausa
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp