Wani abin takaici ya faru a Wawa Cantonment, Jihar Neja, inda ya bar mazauna yankin cikin tashin hankali bayan wani soja da ake zargin ya kashe matarsa kafin ya kashe kansa.
Stephen Nwachukwu, Mataimakin Daraktan Harkokin Jama’a na Sojoji ya bayyana a cikin wata sanarwa da aka fitar.
- JIBWIS FCT Ta Yi Taron Yaye Iyaye Mata Da Suka Kammala Koyon Sana’o’i
- Lewandowski Ba Zai Buga Wasan El Classico Ba
An bayyana cewa Lance Corporal Akenleye Femi, wanda ke aiki a 221 Battalion, Wawa Cantonment, ana zargin shi ne ya aikata wannan mummunan lamari a ranar Asabar.
“Wannan mummunan lamari da ya faru a ranar 11 ga Oktoba, 2025, a Wawa Cantonment, Jihar Neja, ya haifar da yanayi mai cike da tashin hankali, inda mazauna sansanin suka shiga cikin mamaki kan yadda irin wannan abin takaici zai iya faruwa,” in ji wani bangare na sanarwar.
A cewar rundunar sojoji, an gano gawarwakin Lance Corporal Femi da matarsa a cikin gidansu dake gini na 15, daki mai lamba 24, Corporals and Below Kuarters, a cikin sansanin.
Binciken farko ya nuna cewa sojan yana kan aiki a lokacin kuma ya nemi izini daga babban jami’i domin ya kula da wasu harkokin kansa kafin ya dawo aiki.
“Rundunar Sojin Nijeriya tana matukar bakin ciki kan wannan lamari, sannan tana taya iyalan, abokan aiki, da abokan marigayin jimami kan wannan babban rashi.
“Rundunar soji kuma tana addu’ar Allah ya jikansu cikin salama,” in ji Nwachukwu.
An ajiye gawarwakin marigayin, sannan an fara gudanar da cikakken bincike don gano dalilan da suka haifar da wannan abin takaici.
“Brigadier Janar Ezra Barkins, kwamandan 22 Armoured Brigade, ya tabbatar wa jama’a cewa sakamakon binciken zai kasance a bayyane kuma za a duba shi sosai, tare da daukar matakan da suka dace don hana faruwar irin wannan lamari a nan gaba,” in ji Nwachukwu.