Wani mutum dan shekara saba’in a duniya, Apollos Danlami ya rasa ransa yayin da wani kuma mai suna Naemiya Bature mai shekara 65 da wasu adadin mutane suka jikkata a wani rikicin da ya samo asali kan nadin sarautar Hakimin kauyen Sang da ke cikin karamar hukumar Bogoro a jihar Bauchi.
Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi ta cikin sanarwar da ta fitar, inda ta ce, an fara samun rashin jituwar ne sakamakon boren da wasu fusatattun matasa suka yi na kin amincewa da nadin sarautar.
Sanarwar mai dauke da sanya hannun jami’in watsa labarai na hukumar, SP Ahmed Mohammed Wakil, ta ce, a sakamakon rikicin, fusatattun matasan sun banka wa gidaje 64 wuta, kona babura 3, da kadarorin miliyoyin naira sakamakon rikicin.
Sanarwar ta ce, “A ranar 15/04/2023 rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta samu rahoton cewa wani rikici na faruwa a yankin Bogoro. Binciken farko-farko ya nuna cewa rikici ne ya kunno kai a kauyen Sang da ke karamar hukumar Bogoro wanda ya samu asali daga batun nadin sarautar Hakimin Sang.”
Ahmad Wakil ya ce, wasu fusatattun matasa sun fito sun nuna adawarsu da nadin lamarin da ya kai ga juyawa zuwa rikici da har ya janyo mutuwa da jikkata wasu.
Wakil ya kara da cewa a kokarinsu na daukan matakin gaggawa domin shawo kan rikicin da daidaito da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, nan take rundunar ta tura karin jami’an ‘yansanda zuwa yankin domin tabbatar da zaman lafiya.
Sanarwar ta kara da cewa zuwa yanzu dai zaman lafiya ya farfado a yankin kuma dukkanin matakan kariya na tsaro an dauka.
Kan hakan Wakil ne ya sanar da cewa, hukumar na shirye wajen tabbatar da kare rayuka da dukiyar jama’a a kowani lokaci, “Kuma ana cigaba da sintiri a yankin domin tabbatar da wani rikicin bai sake barkewa ba.”
Sanarwar ta nakalto cewa, kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi, CP Aminu Alhassan ya umarci babban jami’in dan sanda a Bogoro da ya kaddamar da bincike domin gano hakikanin abubuwan da suka faru da suka janyo rikicin.
Kazalika, ya kuma ce, dukkanin kokari ya kankama wajen ganin an cafko tare da taso keyar wadanda ke da hannu a janyo wannan rikicin, inda ya ce da zarar aka kamo su to za a gurfanar da su a gaban kotu domin su dandana kudarsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp