A cikin shekarar da ta gabata, sassan duniya da dama sun fuskanci tashe-tashen hankula. Shin duniya za ta fi kyau a shekarar 2025? Ta yaya kasar Sin wadda ta kasance kasa mai tasowa mafi girma, za ta ci gaba da samar da karfi ga duniya?
“Har kullum muna bunkasa ne bisa yadda muke ta daidaita matsalolin da ke gabanmu, kuma muna kara samun karfinmu ne bisa yadda muke ta cin jarrabawar da aka yi mana, don haka, ya kamata dukkaninmu mu yi imani da kanmu.” Ta jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi don murnar shiga sabuwar shekara ta 2025, kasashen duniya sun shaida irin nasarorin da kasar Sin ta samu a shekarar da ta wuce, da ruhin kasar na rashin tsoron wahalhalu da ma niyyarta ta tinkarar matsaloli da cimma burikanta.
- Rahoto: Sana’ar Watsa Labarai Ta Kasar Sin Ta Shiga Zamanin Cudanyar Digital Da Basira
- Kwamitin Kasa Na Majalisar CPPCC Ta Kasar Sin Ya Yi Bikin Maraba Da Sabuwar Shekara
Idan duniya ta yi kyau, to, Sin za ta yi kyau, idan Sin ta yi kyau, to, duniya za ta kara da kyau. Bisa ga dunkulewar duniya, tuni dai Sin da duniya suka kafa alaka ta kut-da-kut, kuma makomarsu na kara zama irin ta bai daya.
Bayan wucewar 2024, shekarar 2025 ta riga ta bayyana ga idon jama’a. “Ya kamata mu aiwatar da kwararan manufofi masu inganci, kuma mu kara mai da hankali a kan inganta bunkasuwar kasa, da kara dogara da kanmu wajen bunkasa kimiyya da fasaha na zamani, don tabbatar da bunkasar tattalin arziki da zamantakewar al’umma cikin yanayi mai kyau.” “Yanzu haka akwai wasu sabbin abubuwan da muke fuskanta a fannin bunkasuwar tattalin arziki, ciki har da rashin tabbas da muke fuskanta daga waje, da kuma matsin lamba da muke fuskanta sakamakon sauyin abubuwan da ke samar da bunkasuwar tattalin arziki, wadanda za mu iya daidaita su idan mun yi kokari”……Jawabin Xi Jinping yana isar da kwarin gwiwa, da daidaita hasashen da kasashen waje suka yi, kana ya aika sakon maraba ga dukkan bangarori, da su ci gaba da more nasarori sakamakon saurin ci gaban kasar Sin.
A shekarar nan ta 2025, kasar Sin na ci gaba da fuskantar kalubale na cikin gida da waje, amma ba za ta ji tsoron hakan ba, tana cike da imanin ci gaba da inganta zamanintarwa iri na kasar Sin, don kara samar da zaman jin dadi ga jama’arta, da ma kara samar da dammamaki ga kasashe daban daban wajen samun bunkasuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp