• English
  • Business News
Sunday, November 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wannan Kyakkyawan Tunani Ya Shafa Ma Hamadar Sahara Launin Kore

by CGTN Hausa and Sulaiman
5 months ago
Sahara

Akwai wani zancen hikima, dake yaduwa a wasu sassan nahiyar Afirka, wanda ma’anarsa ita ce, “A yankin fako a kan samu mutane masu fama da talauci, kana mutanen su ma suna kara fadada wuraren fako.” Wannan magana ta nuna mawuyacin halin da ake fama da shi a wurare masu kusa da yankin hamada, inda ake samun tabarbarewar yanayin talauci, da matsalar sarrafa albarkatu ba bisa ka’ida ba, da lalacewar muhallin halittu, bisa yadda wadannan matsalolin suke wa juna tasiri. Sai dai yanzu an samu damar daidaita wannan yanayi mai wuya, bisa karfafar hadin gwiwar bangarorin Sin da Afirka.

A yau ne na karanta wani bayanin da ya shafi ci gaban aikin gina yankin nuna fasahohin kyautata muhallin halittu na Sin da Afirka, da ake gudanar da shi a kasar Mauritania. An ce, wasu kwararru ‘yan kasar Sin sun gina wani “yankin dausayi” a cikin yankin kasar dake dab da hamadar Sahara, inda suka nuna fasahohin hana kwararar hamada, da tsimin ruwa, da daidaita yanayin kasa don biyan bukatar gudanar da aikin gona, da samar da kayan lambu mai jure yanayin karancin ruwa, da saka na’urorin zamani na ban ruwa ta wutar lantarki da ake samu daga zafin hasken rana, da wadanda ke iya sarrafa kansu wajen samar da ruwa ga kayayyakin gona, da dai sauransu.

Hakika kasar Sin ta kware a fannin daidaita matsalar kwararar hamada, inda ta cika burin dakatar da yanayin lalacewar kasa da Majalisar Dinkin Duniya ta sanya, wasu shekaru 10 kafin lokacin da aka kayyade. Daga baya, kasar ta yi amfani da fasahohinta wajen tallafa wa shirin da kungiyar tarayyar Afirka ta AU ta gabatar na gina “babban shingen itatuwa” a nahiyar Afirka, ta yadda aka rage fadin yankuna masu fama da matsalar kwararar hamada daga kaso 72.31% zuwa 69.23% a yankin Sahel dake Afirka, tsakanin shekarar 2000 da ta 2020.

Yanzu a jihar Kano ta Najeriya, wata cibiyar nazari ta hadin gwiwar Sin da Afirka ta kafa yankin nuna fasahohin hana kwararowar hamada, da na dasa itatuwa masu samar da riba, a kokarin daidaita wasu matsalolin da ake fuskantar, da suka hada da habakar yankin hamada, da raguwar karfin kasa a fannin biyan bukatar aikin gona, da karancin ciyayi, da na ruwa, da dai sauransu.

Wasu mutane su kan yi shakku game da hadin gwiwar da ake yi tsakanin bangarorin Sin da Afirka, inda su kan ce wai “kasar Sin ta fi samun moriya.” Sai dai ya kamata a dubi yadda wadannan kwararru Sinawa suka shiga cikin yankunan hamada na kasashen Afirka, tare da samar da gudunmowa a can. To, mece ce moriyar da suke nema daga aikin?

LABARAI MASU NASABA

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

Hakika abin da suke yi shi ne kokarin cika alkawarin da gwamnatin kasar Sin ta sanya, na taimakon yankunan karkara na kasashen Afirka wajen samun hakikanin ci gaba, inda za a kyautata muhallin rayuwar mutane, da fitar da su daga kangin talauci, maimakon samar da karuwar adadin tattalin arziki kawai.

Kana a bayan manufar ta kasar Sin akwai wani tunani mai muhimmanci da kasar ta rike, wato na “Gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya”. A ganin kasar Sin, dukkan al’ummun kasashe daban daban suna zama a duniya daya, don haka suna da makomar bai daya. Saboda haka ya kamata a lura da bukatun sauran kasashe, da tabbatar da ci gaban mabambantan kasashe na bai daya, yayin da wata kasa ke neman raya kanta. To, yanzu mun ga yadda wannan tunani ya shafa launin kore kan hamadar Sahara, kuma tabbas zai haifar da karin ci gaba ga nahiyar Afirka a nan gaba. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari
Ra'ayi Riga

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

November 6, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki
Ra'ayi Riga

Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

November 4, 2025
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan
Ra'ayi Riga

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

November 4, 2025
Next Post
Wani Injin Jirgi Mai Saukar Ungulu Kirar Kasar Sin Ya Samu Shaidar Amincewa 

Wani Injin Jirgi Mai Saukar Ungulu Kirar Kasar Sin Ya Samu Shaidar Amincewa 

LABARAI MASU NASABA

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

November 9, 2025
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

November 9, 2025
Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

November 9, 2025
Triumph

Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

November 8, 2025
Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

November 8, 2025
Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

November 8, 2025
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

November 8, 2025
Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.