Shugaban kwalejin kiwon lafiyar al’ummar Amurka ta jami’ar Rutgers Mr. Perry Halkitis, ya taba bayyana cewa, ana fuskantar wariyar launin fata game da rarraba alluran rigakafi a kasar.
Yau “duniya a zanen MINA” na zana wani Cartoon game da wannan matsala.
Cibiyar kandagarkin cututtuka ta Amurka, ta ba da kididdiga kwanan baya, wadda ke cewa, mutane masu fama da cutar kyandar biri a kasar, yawancinsu masu tsatson Latin Amurka, da na Afrika ne, wanda suka kai kashi 33% da 28%.
Amma, alal hakika, wannan adadi ya fi yawa a wasu jihohi ko birane. Abin bakin ciki shi ne, al’ummu masu tsatson Latin Amurka da na Afrika, ba su samu isassun alluran rigakafin cutar ba.
Perry Halkitis ya ba da tabbacin cewa, ana fuskantar wariyar launin fata kan rarraba allurar rigakafi. Farar fata sun fi samun allura bisa na masu tsatson Latin Amurka da na Afrika.
A cikin wadannan shekaru da suka gabata bayan barkewar cutar COVID-19 a duniya, al’ummar kananan kabilu a Amurka sun sha fama da rashin adalci a fannin ba da jiyya, abin da ya jawo hankalin mutane sosai.
A halin yanzu kuma, annobar kyandar biri ko monkeypox, na sake yin kashedi kan Amurka da cewa, dole ne a duba matsalar wariyar launin fata.
Rayukan ko wane mutum na da daraja, duk da launin fatansu ya bambanta, kowa na da hakki iri daya a duniya, ciki hadda hakkin samun allurar rigakafin. (Mai zane: MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp