Kwararon roba (condom) abu ne mai tasiri wajen kiyaye samun juna-biyu da ba a shirya masa ba, da cututtukan da ake dauka ta hanyar jima’I (STIs).Â
Duk da muhimmancinsa, rashin fahimta da tatsuniyoyi da ke kewaye da kwararon roban na ci gaba da yaduwa a yankuna daban-daban, ciki har da Arewacin Najeriya. Wannan makala zai yi kokarin warware wadannan tatsuniyoyin tare da karin haske a kan muhimmancin amfanin kwararon roba wajen samar da lafiyan jima’i da jin dadi.
- Gwamnatin Kano Ta Kammala Tsara Tunkarar Matsalar Ambaliyar Ruwa
- Manchester City Ta Fara Kakar Wasa Ta Bana Da Kafar Dama
Jita-jitar Farko: Wai kwararon roba ba ya da tasiri wajen hana yaduwar cututtukan jima’i(STIs).
Sabanin abin da ya shahara, kwararon roba yana da matukar tasiri wajen kare hadarin cututtukan jima’i, wanda ya hada da kanjamau (HIB/AIDS). Idan an yi amfani da shi yadda ya dace kuma akai-akai, kwararon robar yana katangewa, tare da kiyaye watsuwar maniyyi a jikin masu jima’i. Bincike masu yawa sun tabbatar da cewa kwararon roba yana da tasiri kimanin kaso 98 cikin 100 wajen hana yaduwar cututtukan jima’I (STIs) idan an yi amfani da shi yadda ya dace.
Jita-jita ta Biyu: Kwararon roba yana rage jin dadin jima’i.
Wata tatsuniyar da ta yadu ita ce, wai kwararon roba yana rage jin dadin jima’i. Yayin da wasu mutane ke da abin da suka fi gamsuwa a kai, to ra’ayin cewa kwararon roba yana rage jin dadi, a duk fadin duniya, kanzon kurege ne. A gaskiya amfani da kwararon roba yana habaka al’amuran jima’i ta hanyar rage fargabar samun juna-biyun da ba a shirya karbarsa ba, da cututtukan jima’i (STIs). Hakan yana ba wa mutane damar jindadi lokacin jima’i ba tare da jin tsoro ba.
Jita-jita ta Uku: Kwararon Roba na Masu Lalata ne Kawai.
Daya daga cikin kuskuren da ya kamata a yi watsi da shi shi ne yarda da cewa kwararon roba an yi shi ne domin mutane masu aiwatar da jima’i barkatai ko masu alaka na wucin-gadi. To kwararon roba na kowa ne, ba tare da la’akari da matsayin alakarsu ko tarihin jimawan jima’i ba. Kwararon roba yana ba da daman zabi da kuma taimakawa ga mutanen da suke darajanta lafiyan jima’i da abokan tarayyarsu.
Jita-jita ta Hudu: Kwararon Roba ya Saba da Karantarwar Addini.
Addini yana taka muhimmiyar rawa a rayuwar dimbin al’ummar Arewacin Nijeriya. Saboda haka, yana da muhimmanci a fahimci mabanbantan jagororin addini, wadanda suka hada da malaman Musulunci, sun halasta amfani da kwararon roba a matsayin garkuwa daga kamuwa da cututtukan jima’I (STIs) da kuma takaita haihuwa barkatai. Wadannan jagorori sun fahimci muhimmancin dabi’ar ingantacciyar jima’i da kariya ga rayuwa.
Jita-jita ta Biyar: Kwararon roba yana da wuyar samu da kuma karanci
Abin takaici, akwai gurguwar fahimta da ke bayyana cewa kwararon roba yana da wuyar samu ko karancin samu a Arewacin Nijeriya. Ko da a ce za a iya samun takaituwar samuwar sa, to akwai yunkurin gwamnati da kungiyoyin-sa-kai wajen ganin bunkasa wadatuwar kwararon robar. Wasu lokutan ana raba su kyauta a asibitocin kula da lafiya, dakunan ba da magani, da kuma taron wayar da kan jama’a.
Kammalawa:
Warware kullin tatsoniyoyin da ake jingina wa kwararon roba yana da matukar muhimmanci wajen samar da lafiyan jima’i da rage yawaitar haihuwa barkatai da cututtukan jima’i (STIs) a Arewacin Nijeriya. Fahimtar tasirin hakan, yadda yake samar da karin jindadi, da kuma fadada hanyoyin samun kwararon robar zai karfafa wa jama’a wajen yanke hukunci game da neman lafiya wajen yin jima’i. Ta hanyar warware wadannan tatsuniyoyi, za mu iya habaka dabi’ar wayewa, ilimi, da kuma yanayin gudanar da jima’i a Arewacin Nijeriya.
Â
Meerah Shinco, ta rubuto daga Jihar Sakkwato. Ana iya samun ta ta email a: [email protected]