Hukumar da ke kula da gasar Laliga ta kasar Sipaniya ta tsayar da ranar 19 ga watan Maris, a matsayin ranar buga wasan hamayya na El Clasico tsakanin kungiyoyin Barcelona da Real Madrid wasan mako na 26 a filin wasa na Nou Camp.
Kawo yanzu dai Barcelona ce daya a kan teburin gasar La Liga da maki 59 da tazarar maki takwas tsakaninta da Real Madrid ta biyu mai maki 51 wanda hakan ya sa ake ganin idan Barcelona ta dage za ta iya lashe gasar ta bana.
- Da Dumi-Dumi: Sergio Ramos Ya Yi Ritaya Daga Buga Wa Sifaniya Kwallo
- Shugaban NIS Ya Kaddamar Da Ofishin Fasfo Na Zamani A Zariya
Robert Lewandowski na Barcelona shi ne kan gaba a yawan cin kwallaye a La Liga a bana, inda yake da kwallaye 15, sai Karim Benzema na Real Madrid da kwallaye 11, shima dan wasa Joselu na Espanyol.
Real Madrid ta doke Barcelona 3-1 a La Liga ranar 16 ga watan Oktoban 2022 a filin wasa na Santiago Bernabeu kuma Barcelona ce ta dauki Spanish Super Cup a Saudi Arabia ranar 15 ga watan Janairu 2023, bayan doke Real Madrid 3-1 a wasan karshe.
Sai dai kungiyoyin za su fara fafatawa a El Clasico a Copa del Rey wasan farko na dab da karshe ranar 2 ga watan Maris a Santiago Bernabeu sannan daga nan za su fuskanci juna a wasa na biyu a La Liga a kakar nan.
Har ila yau, kungiyoyin guda biyu da babu kamar su a kasar Sipaniya kuma su kece raini a wasa na biyu na dab da karshe a Copa del Rey da za a yi a Camp Nou ranar 5 ga watan Afirilu.