Wasu daga cikin al’ummomin da ke zaune a yankunan Shavon da yankin Di-Nyanvoh dake Jalingo babban birnin jihar Taraba, sun koka kan rashin samun wutar lantarki har na tsawon watanni shida.
Sun roki mahukuntan Kamfanin tura wutar na (YEDC) da ya dawo masu da wutar, inda suka yi nuni da cewa, rashin samur wutar ya jefa su da yankunan su cikin hali mawuyaci.
Daya daga cikin mazauna yankin, Sunday Uche ya ce, tun bayan konewar ma’ajiyar wutar Lantarkin (Transformer), watanni shida da suka gabata, sun kasance suna zama a cikin duhu, inda ya ce, hakan ya janyo wasu bata gari, yin amfani da damar wajen aikata wasu manyan laifuka.
Acewar wata mazauniyar Yankin, Mama Toyin ta ce, har ta manta tsawon lokacin da ta sha ruwa mai sanyi a gidan ta, inda ta ce, kamfanin ya mayar da yankunan su, tamkar wani kasurgumin jeji.
Mazauna yankin Shavon, sun ce, sun yi dukkan mai yiwuwa domin kamfanin ya canza masu wata sabuwar Tiransfoma amma hakan ya ci tura.
Da aka tuntubi jin ta bakin Kamfanin mai kula da wutar yankin, wani babban ma’aikaci a kamfanin ya ce kamfanin ya tura bukatar samun wasu Tiransfoma daga Hedikwatar kamfanin dake Yola a jihar Adamawa.
Ya ce, kamfanin na sane da halin rashin wutar lantarkin da al’ummomin ke fuskanta, inda ya ce, mahukuntan a kamfanin na aiki ba dare ba rana domin a sake dawo wa da al’ummomin wutar.
.