• Leadership Hausa
Friday, August 12, 2022
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result
Home Al'ajabi

Wasu Boyayyun Abubuwa Da Ba A Sani Ba Game Da Duniyar ‘Mars’

by Rabi'u Ali Indabawa
4 weeks ago
in Al'ajabi
0
Mars
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Mars ita ce duniya ta hudu daga rana. Ganin cewa duniyar na da launin ja mai kama da jini, Romawa sun yi wa duniyar lakabi da ubangijin yakinsu na wancan lokaci.

Gaskiyar ita ce Romawan sun kwaikwayi mutanen Girka na zamanin baya wadanda suka saka wa duniyar ta Mars sunan ubangijin yakinsu wato Ares.

  • Gwamnatin Kano Ta Rufe Makarantun Kiwon Lafiya 26 Saboda Rashin Lasisi

Sauran al’ummomi na mutanen farko su ma sun bai wa duniyar suna dangane da launin ta – Misali, mutanen Masar sun saka wa duniyar Mars suna “Her Desher,” ma’ana “Ja,” haka su ma ‘yan sama jannti na kasar China na wancan lokacin sun yi mata lakabi da “tauraruwa mai wuta.”
A cikin duniyar ta Mars, launin kasar da ke shimfide launi ne mai kama da tsatsa, wanda alama ce da ke nuna cewa duniyar na da sinadarin iron narke a kasar.

Kasar duniyar da muke ciki na kama da ta Mars duk da cewa tana dauke da sinadarai wadanda ke cikinta tun asali.
Kamar yadda hukumar NASA ta bayyana, sinadarin iron da ke cikin kasar sukan yi tsatsa wanda hakan ke sa kasar duniyar ta Marsa ta koma jajir.

Duniyar Mars kuma na da tsauni mafi girma da zurfi, kuma ita ce ke da kwari mafi tsawo a duniyoyi. Olympus mons katafaren dutse ne mai aman wuta da ke cikin duniyar Mars wanda yake da tsawon kilomta 27, wanda ya yi tsawon tsaunin Everest haka kuma kwarin Balles Marineris wanda aka saka wa suna bayan binciken da jirgin sama jannati na Mariner line ya yi a 1971 – ya kai zurfin kilomita goma haka kuma ya yi tsawon kusan kilomita dubu hudu, wanda hakan na nufin ya yi kashi daya bisa biyar na na nisan Mars kuma ya yi fadin Australia.

Labarai Masu Nasaba

Yadda Mai Wanke-wanke Ta Zama Mataimakiyar Shugaban kasa

Wata Sabuwa: Za A Fara Cin Tarar Mata Kan Kin Aure A Chadi

Haka kuma duniyar Mars ita ce ke da dutse mai aman wuta mafi girma a duka duniyoyi, wato Olympus Mons. Dutsen na da tsawon kilomita 27.

Yanayin zafi ko sanyi na duniyar Mars
Duniyar Mars ta fi duniyarmu ta Earth sanyi matuka sakamakon nisan da duniyar ta Mars take da shi daga Rana. Matsakaicin yanayin da ake samu a Mars ya kai kasa da maki 60 a ma’aunin celcius (-60).

Mars na da iskar carbon diodide mai matukar yawa wanda kaurinsa yana kasa da namu a nauyi, sai dai kaurin na iskar bai kai ya samar da yanayi kamar irinsu hadari da iska ba.

Yanayi na sararin samaniyar Mars yana sauyawa a lokacin da hunturu ke tursasa wa carbon diodide ya bar sararin samaniyar Mars.

A baya, sararin samaniyar duniyar ta Mars na da nauyi matuka kuma yana har ruwa yana iya tafiya a kan duniyar. Bayan wani lokaci, abubuwa marasa nauyi a sararin samaniyar Mars sun gudu sakamakon karfin iskar da ke tahowa daga rana wanda hakan ya yi tasiri ga sararin samaniyar duniyar ganin cewa Mars ba shi da karfin maganadisu na rike abubuwa.

Yanayin zagaye rana
Mars na da matukar nisa daga rana fiye da duniyar Earth, wannan na nufin duniyar ta Mars na da shekara mai tsawo – kwanaki 687 a duk shekara kenan idan aka kwatanta da kwanaki 365 na duniyarmu.

Duka duniyoyin suna da tsawo daya a yanayin dare da rana sai dai yana daukar kusan sa’o’i 24 da mintuna 40 ga duniyar ta Mars ta kammala zagayawar da take yi a duk rana idan aka kwatanta da duniyar Earth mai sa’o’i 24.

Yanayin juyawar da Mars ke yi na kama da na Earth. Hakan na nufin kamar duniyar Earth, adadin hasken ranar da ke sauka a wasu sassa na Mars zai sha bamban a duk shekara sakamakon yanayin zafi da sanyi Mars.

Sai dai yanayin zafi da sanyi na Mars ya wuce na Earth sakamakon siffar duniyar ya fi zama kamar kwai a maimakon kwallo irin yadda Earth take, wanda hakan ya sa zagayawar da da take yi wa rana ya fi tsayi idan aka kwatanta da yadda sauran duniyoyin suke zagaye rana.

A lokacin da Mars ta fi kusa da rana, bangaren Kudancin duniyar na kallon tauraron duniyarmu, wanda hakan ke bai wa duniyar yanayin zafi gajere, sai kuma Arewacin kasar yana fuskanatar yanayin sanyi gajere.

Girma
Mars na da fadin kilomita 6,791 — ta fi duniyarmu ta Earth kankanta wadda ke da fadin kilomita 12,756.
Mars na da matukar girma kamar da kashi 10 cikin 100 na duniyarmu wanda kuma karfin maganadinsun Mars ya kai kashi 38 cikin 100.

Misali mutum mai nauyin kilo 62 a nan duniyar ta Earth idan ya je Mars ba zai wuce kilogram 62 ba amma girma zai zama daya a duka duniyoyin.

Yanayi
Kamar yadda hukumar da ke kula da sararin samaniya ta duniya ta bayyana, duniyar Mars na dauke da kashi 95.32 na sinadarin carbon diodide sai kashi 2.7 na nitrogen da kashi 1.6 na argon da kashi 0.13 na odygen da kashi 0.08 na carbon monodide da adadi kadan na ruwa da nitrogen odide da neon da hydrogen-deuterium-odygen da krypton da denon.

Amma yanayi na duniyarmu ta Earth na dauke da kashi 78 na sinadarin nitrogen da kashi 21 na Odygen da kashi 0.9 na argon da kashi 0.1 na sauran sinadarai.
Wani adadi kalilan na carbon diodide da methane da neon da sauran sinadarai suke da kashi 0.1.

Sinadarai
Duniyar Mars na da sinadaren Iron da nickel da sulfur. Mayafin da ya rufe Mars na kama da wanda ya rufe duniyar Earth wanda akwai dutse wanda ya kunshi silicon da odygen da iron da magnesium.
Yadda kasar Mars take akwai duwatsu irin masu aman wuta wadanda akwai irinsu a duniyar Earth da kuma duniyar wata. Duniyar Earth kuma ta fi kunsar sinadarin earth da kashi 32.1 cikin 100 sai kuma odygen da kashi 30.1 cikin 100 sai silicon kashi 15.1 da magnesium da kashi 13.9 da sulfur da kashi 2.9 da nickel mai kashi 1.8 sai calcium da kashi 1.5 da alminum da kashi 1.4 sai sauran kason 1.2 ya kunshi sauran sinadarai.

ShareTweetSendShare
Previous Post

Rufe Iyakoki Ya Yi Amfani Saboda Mutane Na Cin Shinkafar Gida Yanzu – Buhari

Next Post

El-rufai Ya Amince Da Daukar Karin Malamai 10,000

Related

Yadda Mai Wanke-wanke Ta Zama Mataimakiyar Shugaban kasa
Al'ajabi

Yadda Mai Wanke-wanke Ta Zama Mataimakiyar Shugaban kasa

7 hours ago
Wata Sabuwa: Za A Fara Cin Tarar Mata Kan Kin Aure A Chadi
Al'ajabi

Wata Sabuwa: Za A Fara Cin Tarar Mata Kan Kin Aure A Chadi

2 days ago
Mahaifiyata Ta Sare Min Hannaye Haka Siddan – Budurwa
Al'ajabi

Mahaifiyata Ta Sare Min Hannaye Haka Siddan – Budurwa

5 days ago
Wasu Nau’in Kwadi Da Macizai Sun Haddasa Asarar Dala Biliyan 16 A Duniya
Al'ajabi

Wasu Nau’in Kwadi Da Macizai Sun Haddasa Asarar Dala Biliyan 16 A Duniya

5 days ago
An Kama Wani Mutum Yana Jima’i Da Akuya A Ogun
Kotu Da Ɗansanda

An Kama Wani Mutum Yana Jima’i Da Akuya A Ogun

7 days ago
Yadda ‘Yan Sa-kai Suka Lakada Wa Alaramma Duka Har Lahira A Kano
Al'ajabi

Yadda ‘Yan Sa-kai Suka Lakada Wa Alaramma Duka Har Lahira A Kano

1 week ago
Next Post
El-rufai Ya Amince Da Daukar Karin Malamai 10,000

El-rufai Ya Amince Da Daukar Karin Malamai 10,000

LABARAI MASU NASABA

Kungiyar Kawance Ta Sin Da Niger Na Goyon Bayan Manufar Sin Daya Tak

Kungiyar Kawance Ta Sin Da Niger Na Goyon Bayan Manufar Sin Daya Tak

August 12, 2022
Da Dumi-Dumi: ‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sace Buhari Da El-Rufai 

Rashin Tsaro Na Kawo Koma Baya Ga Tattalin Arzikin Nijeriya – Buhari

August 12, 2022
Wang Wenbin: Duk Irin Sauyin Yanayi Sin Za Ta Wanzar Da Fadada Bude Kofa

Wang Wenbin: Duk Irin Sauyin Yanayi Sin Za Ta Wanzar Da Fadada Bude Kofa

August 12, 2022
Shugaba Xi Ya Yi Kira Ga Sassan Kasa Da Kasa Da Su Yi Hadin Gwiwar Samar Da Ci Gaban Duniya

Shugaba Xi Ya Yi Kira Ga Sassan Kasa Da Kasa Da Su Yi Hadin Gwiwar Samar Da Ci Gaban Duniya

August 12, 2022
Zan Biya Wa ASUU Bukatunsu Idan Na Zama Shuagaban Kasa – Atiku

Zan Biya Wa ASUU Bukatunsu Idan Na Zama Shuagaban Kasa – Atiku

August 12, 2022
Hanyoyin Jiragen Kasa Da Sin Ta Gina Sun Zama Shaidar Raya Shirin “Ziri Daya Da Hanya Daya”

Hanyoyin Jiragen Kasa Da Sin Ta Gina Sun Zama Shaidar Raya Shirin “Ziri Daya Da Hanya Daya”

August 12, 2022
Yunkurin Amurka Kan Sana’ar Kera Sassan Na’urorin Laturoni Ba Zai Yi Nasara Ba

Yunkurin Amurka Kan Sana’ar Kera Sassan Na’urorin Laturoni Ba Zai Yi Nasara Ba

August 12, 2022
Hisbah Ta Jadadda Muhimmancin Gwajin Lafiya Kafin Aure 

Hisbah Ta Jadadda Muhimmancin Gwajin Lafiya Kafin Aure 

August 12, 2022
Shugaba Buhari Zai Kawo Karshen Rashin Tsaro A Nijeriya -Buratai

Shugaba Buhari Zai Kawo Karshen Rashin Tsaro A Nijeriya -Buratai

August 12, 2022
Gwamnatin Tarayya Ta Ware Biliyan 2.6 Domin Tsaron Abuja

Daga Asabar 8 Zuwa Talata 11 Ga Watan Muharram 1444

August 12, 2022
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.