ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, July 5, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wasu Daga Cikin Manhajojin Da Ke Bata Wayar Android

by Ibrahim Sabo
3 years ago
Android

Kamar yadda kowa ya sani wayar Android ana loda mata manhajoji (Applications) iri daban-daban. Idan aka ce ‘App’ wato (application) ko ‘Apk’ wato

(Android Package Kit) shi ne abubuwan da wayar Android take amfani da shi don saukake aiki da wayar wajen yin amfani da ita kai tsaye ga abin da kake so ka sarrafa a wayarka. Sannan applications ana saka su a waya har ma ana iya tura wa a wasu Android din.

  • GORON JUMA’A
  • Akidar Siyasar Malam Aminu Kano Da Ta ‘Yan Siyasar Yanzu A Mizani –Farfesa Habu

Duk wayar Android tana bukatar manhajoji don tafiyar da ita cikin sauki, domin sune za su taimaka wa mai amfani da wayar wajen jin dadin amfani da ita.

ADVERTISEMENT

Akwai Applications masu yawan gaske da mai Android zai iya amfani da su kamar irin na Banki, Chat, Music, Browsers, Game, da na Karatu da sauransu. Amma kuma bayan wadannan Apps din wadanda suke da matukar amfani ga mai wayar Android, sannan kuma akwai wadanda suke ba su da amfani sosai, sai dai ma a ce cutar da wayar suke maimakon amfanarwa.

Ire-Iren wadannan Manhajojin masu cutarwa, iri biyu ne. Akwai masu cutarwa kaitsaye da kuma masu cutarwa a hankali-hankali ba tare da mai amfani da wayar ya sani ba. Irin wadannan sun hada

LABARAI MASU NASABA

Gasar Kofin Duniya: Ko Morocco Na Iya Tsallake Tarkon Faransa?

Kwankwasiyya Ta Buƙaci A Binciki Zargin Kasafin Kuɗin PFIPC

UC Browser-

UC Browser yana daya daga cikin shahararrun ‘applications’ da ake yawan amfani da su a wayar Android. Play store ya bayyana cewa an sauke (download) fiye da miliyan 500, dalili kuwa bai wuce saurin sauke abu da yake yi da wuri ba, da kuma ci gaba (acceleration) da yake da shi, da kuma kyakkyawan shafi mai tsari.

Bayan amfanin da yake da shi, akwai matsaloli kamar haka:

-Yana daukar bayanai kamar contacts, SMS da location.

-Ana tuhumarsu da sayar da bayanan sirri na mutanen da ke amfani da shi a wasu mutane a waje, kamar IMEL, IMSI da wasu bayanan ga kamfanin ALIBABA, ba tare da izinin mai wayar ba kuma babu tsaro (encryption).

To don haka kuwa bayananka za su fita waje zuwa ga wasu mutane da za su iya maka kutse (hacking), su sace password dinka ba tare da ka sani ba.

Clean Master:

Manhajar Clean Master akwai bayanai masu ba da mamaki, domin kuwa yana da ‘rebiews’ a play store wajen miliyan 43 (duk da akwai wasu kamfanonin Apps dake biyan kudi don su samu (rebiew) din.

Shi wannan applications din kamfaninsa ya yi alkawarin zai taimaka wa mai amfani da shi wajen goge abubuwan da ba su da amfani (junk files) a ma’adana (memory), da kuma da bawa waya damar samun sarari (space), da kuma karin sauri wajen shiga yanar gizo (Internet browsing).

Matsalar da ake samu da shi ba wani na damuwa ba ne sosai, sai dai duk ayyuka da yake yi sabbin wayoyin Android suna dauke da shi, ba ka bukatar sai ka saka application mai yin irin wannan aikin.

Idan kana bukatar goge ire-iren wadannan abubuwa marasa amfani, ka bi wadannan matakan daga wayarka;

Settings>Apps>Storage >Clear Cache… Shikenan ka samu lafiya.

Sannan kuma idan ka kunna datarka, zai rika fito da wasu shafuka (ads) wadanda ba ka da alaka da su, sai dai su cinye maka datar kuma su hana wayarka sauri wajen yin browsing, kuma yana adana wadannan bayanai a cikin wayarka a boyayyen waje ba tare da ka sani ba, a cikin ma’adanarka (memory).

Du Battery Saber

Du Battery Saber: tun wajen shekarar 2012 aka kirkiro wannan application din, kuma ya samu karbuwa sosai, domin an  sauke shi (downloading)fiye da miliyan 100, daga play store. Sannan kuma masu App din sun yi shi ne don ya taimaka wajen yin cajin Batirin waya da sauri (fast charging), da kuma sanya waya yin sauri (speed). Amma wannan duk yaudara ce kawai, domin abubuwan da ke sanya waya saurin caji sune kamar haka:

-Ya zamanto wayarka tana goyon bayan caji da sauri (support fast charging)

-Amfani da caja mai sauri musamman wanda waya ta zo da shi.

Amma babu wani application da zai sa wayarka saurin yin caji.

Wata matsala kuma ita ce, wannan application din a kowane lokaci a bude yake, wanda hakan na jawo shanyewar cajin waya maimakon ragewa, kuma yana amfani da datar wayarka in dai a bude yake, wajen fito da shafukan da ba ka bukata (ads) da za su iya sa wayarka tana yin rashin sauri (slow). Duk wasu applications da ke nuna za su taimaka maka wajen rage shan Batir, ko sa wayarka sauri (speed), ko rage fili (space) a ma’adana (memory), ba su da amfani, tun da an yi wayoyi masu rike caji sosan gaske.

Es File Explorer

Shi wannan application din, masu amfani da shi za su yi mamaki idan aka ce musu yana daga applications masu matsala. Ba don komai ba sai don amfaninsa ga mai wayar Android da kuma yadda mutane suka tasirantu da shi.

A wannan zamanin, sabbin wayoyi da ke fitowa sun zo da irin tsarin da wannan application din yake dauke da shi, ba ka da bukatarshi a yanzu, sai dai ya cike maka ma’adana (memory) kawai.

To shi ma yana da matsaloli kamar haka:

-Yana bullo da shafukan talla (ads) da kanshi

-Yana tura bayanai ga wasu wurare ba tare da izini ba, wanda hakan na ba da dama ga masu kutse (hackers) su shiga su maka barna a wayarka.

Idan har ka matsa da yin amfani da ‘file manager app’, to ka yi amfani da ‘FILE GO’ wanda kamfanin GOOGLE masu manhajar ANDROID suka kirkiro, ya fi inganci da kuma tsaro a wayarka.

Anti Virus Apps

Kusan duk application da ke da tsarin anti birus suna da mantsaloli da yawa fiye da amfanarwa. Ga shi kuma mutum da zarar ya sayi waya, tunanin farko shi ne saka anti birus akan wayar, domin samun ingantaccen tsaro. Abin da mutane ba su sani ba shi ne tsarin manhajar Android (operating system) ya yi daban da tsarin manhajar (windows) na’ura mai kwakwalwa (computer). Manhajar Android ba ta bukatar anti birus don samun kariya da kuma tsaro ga waya.

Kusan duk apps na anti birus sukan tambayi izini (permission), bayan an ba su, sukan samu cikakken dama (access) ga dukkan bayanai da ke cikin wayarka tun daga kan kira (calls), sakonni (messages), bayanan sauran apps din da ke wayarka, da passwords, da kuma duk wasu ajiyayyun fayil (file) a wayarka, kuma sukan tura irin wadannan bayanai ga wasu kamfanoni ba tare da izinin mai wayar ba.

Idan kana bukatar wayarka ta samu fili (space), kuma ta daina zafi (heat), da nauyi (delay) to ka kauracewa irin wadannan apps din na anti birus. Akwai application a Google Play store mai suna PLAY PROTECT FUNCTION, ka sauke shi, ka installing dinsa a wayarka, to za ka samu tsaro mai inganci, domin masu manhajar Android wato Google su suka kirkiro shi.

Android
Ibrahim Sabo
+ postsBio
  • Ibrahim Sabo
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-sabo/
    Sabuwar Hanyar Kwacen Shafin Facebook (II)
  • Ibrahim Sabo
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-sabo/
    Sabuwar Hanyar Kwacen Shafin Facebook (I)
  • Ibrahim Sabo
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-sabo/
    Mene Ne Tsarin 5G?
  • Ibrahim Sabo
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-sabo/
    Yadda Ake Sarrafa Rubutu Ta Word-Processing

MASU ALAKA

Gasar Kofin Duniya: Ko Morocco Na Iya Tsallake Tarkon Faransa?
Manyan Labarai

Gasar Kofin Duniya: Ko Morocco Na Iya Tsallake Tarkon Faransa?

July 5, 2026
Kwankwasiyya Ta Buƙaci A Binciki Zargin Kasafin Kuɗin PFIPC
Manyan Labarai

Kwankwasiyya Ta Buƙaci A Binciki Zargin Kasafin Kuɗin PFIPC

July 4, 2026
Kano Pillars Ta Naɗa Mataimakin Kocin Super Eagles, Daniel Ogunmodede A Matsayin Sabon Kocinta
Manyan Labarai

Kano Pillars Ta Naɗa Mataimakin Kocin Super Eagles, Daniel Ogunmodede A Matsayin Sabon Kocinta

July 3, 2026
Next Post
Babu Barazanar Kai Hari A Kano – ‘Yansanda

DPO Ya Yanke Jiki Ya Fadi, Ya Rasu A Jigawa

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Rasha Za Su Gudanar Da Atisayen Sojojin Ruwa Da Sintiri Na Hadin Gwiwa

Sin Da Rasha Za Su Gudanar Da Atisayen Sojojin Ruwa Da Sintiri Na Hadin Gwiwa

July 5, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan ‘Ƴan Nijeriya 2 A Afrika Ta Kudu

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan ‘Ƴan Nijeriya 2 A Afrika Ta Kudu

July 5, 2026
Tawagar Jami’an Lafiya Ta Sin Ta Kafa Cibiyar Horar Da Ma’aikatan Jinya A Saliyo

Tawagar Jami’an Lafiya Ta Sin Ta Kafa Cibiyar Horar Da Ma’aikatan Jinya A Saliyo

July 5, 2026
Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (2)

July 5, 2026
Sin Ta Sha Alwashin Karfafa Musaya Da Sweden A Dukkanin Fannoni

Sin Ta Sha Alwashin Karfafa Musaya Da Sweden A Dukkanin Fannoni

July 5, 2026
Messi Da Mbappé Na Jagorantar Cin Ƙwallaye A Gasar Kofin Duniya

Messi Da Mbappé Na Jagorantar Cin Ƙwallaye A Gasar Kofin Duniya

July 5, 2026
Adadin Mutanen Da Tsananin Zafi Ya Kashe A Turai Ya Haura Dubu 1,300 —WHO

Adadin Mutanen Da Tsananin Zafi Ya Kashe A Turai Ya Haura Dubu 1,300 —WHO

July 5, 2026
Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Taimakon Ƙasashen Waje

Kafa Cibiyar NIPHID: NCDC Ta Yi Kuskuren Fahimtar Ƙudirin Dokar

July 5, 2026
Dalilan Da Suka Jawo Aka Ƙi Yin Maraba Da FIM House A Jihar Kano

Dalilan Da Suka Jawo Aka Ƙi Yin Maraba Da FIM House A Jihar Kano

July 5, 2026
Lampard Zai Ci Gaba Da Zama A Coventry City

Lampard Zai Ci Gaba Da Zama A Coventry City

July 5, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.