Har yanzu akwai sauran rina a kaba a cikin jam’iyya mai mulki ta APC, domin kuwa akwai jiga-jigan APC da har yanzu ba a ji duriyarsu ba a wurin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tun bayan watanni bakwai da jam’iyyar ta gudanar da zaben fid da gwani da tsohon gwamnan Jihar Legas ya lashe, alamun na nuna cewa ‘yan takara shida daga cikin 14 har yanzu akwai sauran rina a kaba.
‘Yan takarar da ke tsammani su bayar da gudummuwa wajen samun nasarar jam’iyyar a jihohinsu, amma suna nuna halin-ko-in-kula kan yakin neman zaben jam’iyyar.
Tinubu dai ya samu kuri’u a zaben fitar da gwani guda 1,271, yayin da ya doke sauran ‘yan takara 13 da suka hada da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da shugaban majalisan dattawa, Ahmad Lawan wadanda suka samu kuri’u 316, 235 da kuma 152.
Suran ‘yan takaran sun hada da Ogbonnaya Onu wanda ya samu kuri’a daya da Rochas Okorocha wanda bai samu kuri’a ko daya ba da Dabe Umahi wanda ya samu kuri’u 38 da Yahaya Bello da ya samu kuri’u 47 da Tein Jack-Rich wanda bai samu komi ba da Fasto Tunde Bakare wanda bai samu komi ba da Emeka Nwajiuba wanda ya samu kuri’a 1 da Ahmed Sani Yarima wanda ya samu kuri’u hudu da Farfesa Ben Ayade da ya samu kuri’u 37 da kuma Ikeobasi Mokhelu wanda bai samu komi ba.
Tun watanni uku da fara kamfen din Tinubu ba a ga Osinbajo, Amaechi, Onu, Okorocha, Bakare da kuma Nwajiuba a wurin yakin neman zaben APC ba.
A cikin watan Agusta, daya daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa, Nicolas Felid ya gudanar da ganawa domin hada kan dukkan ‘yan takara wuri guda, amma kuma suka kaurace wa taron.
Yayin da Amaechi, Onu da kuma Bakare suna cikin kwamitin yakin neman zaben Tinubu, sai dai kuma Osinbajo, Okorocha da kuma Nwajiuba babu sunayensu a ciki.
Duk da saka sunayen Amaechi, Onu da Bakare amma ba a ji duriyarsu a dukkan gangamin jam’iyyar wanda a yanzu ya rage kasa da kwanaki 45 a gudanar da zaben shugaban kasa.
Osinbajo
Bincike ya nuna cewa har yanzu Osinbajo bai halarci kamfen din Tinubu ba. Wannan lamari yana ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce kan cewa har yanzu jiga-jigan ‘yan siyasan guda biyu na jam’iyya mai mulki ba su yi sulhu ba tun bayan kammala zaben fitar da gwani na shugaban kasa a jam’iyyar.
Ko a ranar 10 ga watan Juni sai da dan takarar shugaban kasan ya ziyarci mataimakin shugaban kasa a gidansa da ke Aguda a Abuja, bayan kwanaki kadan da Osinbajo ya taya shi murna lashe zaben fitar da gwani tare da yin alkawarin zai yi aiki da shi domin samun nasarar lashe babban zabe.
Ziyarar ta zo ne bayan da aka ce Tinubu ya yi watsi da mataimakin shugaban kasa duk da ki mikewa da ya yi wajen tarbar sa a wurin taron babban jam’iyyar, inda ya fi mayar da hankali kan shugaban majalisan wakilai, Femi Gbajabiamila.
Dangane da rashin samun sunan mataimakin shugaban kasa a kwamitin kamfen kuwa, kakakin kwamitin yakin neman zaben, Festus Keyamo ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya bukaci kar a saka sunan Osinbajo da sakataren kwamnatin tarayya, Boss Mustapha a cikin kwamitin saboda su mayar da hankaili kan harkokin tafiyar da gwamnati.
A ranar 21 ga watan Disambar 2022, Osinbajo ya ziyarci Tinubu a gidansa da ke Abuja tare da mataimakin takararsa, Sanata Kashim Shattima, bayan da ake ta yada jita-jitar cewa rashin halartarsa yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa ya samo asali ne sakamakon raba gari da suka yi da shi.
Majiya mai tushe ta ce ziyarar ba don wata manufa ta siyasa ba ce illa ta sada zumunci saboda daddiyar dangantakar da ke tsakaninsu. Ta kara da cewa ziyarar ta kasance martani ne kan ziyarar da Tinubu ya kai wa mataimakin shugaban kasan bayan kammala zaben fitar da gwani.
Amaechi
Har ila yau, wanda ake ganin ya bace daga kwamitin kamfin din Tinubu shi ne, tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi wanda shi ne ya zo na biyu a zaben fid da gwani na shugaban kasa a jam’iyyar APC. Duk da dai an nada shi a matsayin mai bayar da shawara ta musamman kan abubuwan more rayuwa a kwamitin kamfen din Tinubu, amma kuma ba a taba ganinsa a wurin gangamin yakin neman zaben ba. Shi ne daraktan kamfen din Shugaba Buhari har sau biyu a 2015 da 2019. Tsohon gwamnan Jihar Ribas ya kaurace wa fitowa bainar jama’a tun lokacin da Tinubu ya kayar da shi.
Mai taimaka wa tsohon ministan ya ce Tinubu bai yi wa ubangidansa adalci ba. “Abun kunya ne a yi wa Amaechi rashin adalci. Domin a lokacin da Oshiomhole ya ziyarci Fatakwal, ya bukaci mutane su goyi bayan Tinubu, sannan a sauran mukaman kuma su goyi bayan Wike. Haka kuma an sake maimaita irin wannan lamari a lokacin da gwamnan Jihar Ebonyi ya ziyarci jihar,” in ji shi.
Onu
Tsohon ministan kimiyya da fasaha da kere-kere, Dakta Ogbonnaya Onu, shi ma ya yi batan-dabo daga yakin neman zaben Tinubu.
Onu ya kasance jigo a APC wanda ya yi takarar samun tikitin kujerar shugaban kasa a watan Yuni, inda ya fice daga wurin zaben fid da gwani na babban taron jam’iyyar da yake ganin babu adalci a cikin shugabancin jam’iyyar.
Ya kasance a sahun gaba wajen fafutukar ganin an kai takarar shugaban kasa ga yankin kudu maso gabashin Nijeriya.
Lokacin da aka tuntubi daya daga cikin masu taimaja wa Onu, ya bayyana cewa yana yin abin da ya kamata a bayan fage, domin ba wajibi ba ne a rika ganinsa a filin kamfen ko da yaushe.
“Lokacin zabe 2015 da 2019, ba a ganinsa a ko da yaushe wajen yakin neman zabe, amma yana daga cikin yakin neman zabe wanda ya gabatar da abin da ya kamata a sirrance.
“Shi mutum ne mai mutunci, baya fitowa fili wajen gudanar da abubuwansa. Baya canzawa daga wani rashin adalci da aka yi masa,” in ji shi.
Bakare
Duk da an saka sunan Fasto Tunde Bakare daga cikin mambobin kwamitin yakin neman zabe, ya barranta da lamarin tun lokacin da aka fara gudanar da kamfen.
Wata majiya da ke kusa da Bakare ta bayyana cewa yana na kan bakansa kan shi ne shugaban kasan Nijeriya na 16, bai canza matsayinsa ba duk da cewa har yanzu yana kokarin yadda mafarkinsa zai tabbata lokacin da baya takara.
Majiyar ta ce Bakare ya kaurace wa ganawar ‘yan takarar shugaban kasa wanda daga baya aka dage zuwa watan Satumbar 2022, wanda ba a gudanar ba. Majiyar ta kara da cewa Fasto Bakare ya samu wannan gayyata ne a hannun daya daga cikin mataimakansa, ya ji babu dadi da aka kira wannan taro a daidai lokacin da aka kasa magance matsalolin da suka turnuke babban taron jam’iyyar.
“Kamar yadda ake yi, faston bai shiga yakin neman zaben ba kuma bai taba bai wa mabiyansa shawara ba kan su zabi wanni dan takara,” in ji majiyar.
Amma a watan Yuli, Bakare ya yi watsi da tikitin takarar musulma da musulmi na APC, inda ya ce mutane su mayar da hankali kan gina kasa.
Nwajiuba
Tsohon karamin ministan ilimi, Barista Chukwuemeka Nwajiuba ba a ji duriyarsa ba a dukkanin gangamin yakin neman zaben Tinubu tun lokacin da aka fara a shekarar bara.
Nwajiuba ya dai samu kuri’a daya ce a zaben fitar da gwani na APC, ana kyautata zaton ya shigar da kararraki guda biyu kan jam’iyyar.
A karar da ya shigar a babban kotun tarayya da ke Abuja na neman a maye gurbin Tinubu a matsayin dan takarar shugabab kasa a jam’iyyar APC, saboda bai cika wasu sharudda da sashi na 90 (3) da dokar zaben shekarar 2022 ta gindaya ba, a watan Disamba ne kotun ta yi watsi da karar, sakamakon dokar hana shigar da kara a cikin kwanaki 14 kan dalilin daukar matakin a karkashin sashi na 285 (9) na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999.
Hakazalika, wata kotu a baya ta yi watsi da karar da Nwajiuba ya shigar ta wata kungiya mai zaman kanta, inda take neman a dakatar da Tinubu da dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar bisa zargin karya dokar zabe da kawo tashin-tashina a zaben fitar da gwani da kuma sayen kuri’u.
Ina Nan A APC – Okorocha
Tsohon gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha wanda bai samu ko kuri’a guda ba a zaben fid da gwani baya cikin kwamitin yakin neman zabem jam’iyyar. Jigon APC ya ce zai yi iya bakin kokarinsa na ganin cewa jam’iyyar ta samu nasara.
“Ina iya bakin kokarina, kamfen baya ta’allaka ba ne ga gudanar da gangami ba. Akwai hanyoyi da dama na gudanar da yakin neman zabe. Ina nan a APC, kuma ba zan taba barin APC ba,” in ji shi.
A martanisa na rasa saka sunansa a kwamitin kamfen kuwa, Okorocha ya ce, “Ni na damu ne da soyayyar da nake yi wa kasata da kuma jam’iyyata, ba na bukatar rike wani matsayi a kwamitin kamfen din APC ko kuma na wata jam’iyya. Wadannan abubuwan duk ba su da muhimmanci.
“Mun fahimci cewa siyasa na da kaskanci. Zan bayar da sanarwa kan wannan lamari nan ba da jimawa ba.”