Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa surutan da wasu ke yi kan cewa ta ƙi bin umarnin kotu dangane da rikicin shugabancin jam’iyyar APGA wani yunƙuri ne na ɓata mata suna.
Babban Kwamishina kuma shugaban Kwamitin Wayar da Kan Masu Zaɓe na hukumar, Lauya Festus Okoye, ya faɗi a wata sanarwa ga manema labarai cewa hukumar ta lura da yadda wata ƙungiya da ba a gane kan ta ba ta ke yamaɗiɗi kan al’amarin, ta na rarraba fastoci da yin surutai inda ta ke zargin hukumar da ƙin bin umarnin Kotun Ƙoli da ya ce wai wani mai suna Cif Edozie Njoku ne “Shugaban APGA na Ƙasa na gaskiya”.
Hukumar ta ce ana yaɗa waɗannan fastocin da surutan ne don kawai a yi wa INEC sharri da nufin a yaudari waɗanda ba su san gaskiyar abin da ke faruwa ba.
Okoye ya ce: “Mu na so mu bayyana cewa waɗannan al’amurra fa sun shafi faɗin gaskiya ne tare da bin doka da oda ba wai kwakwazo da neman tada zaune tsaye ba.
“A lura da cewa ƙarar da aka kai kotu ta samo asali ne daga Babbar Kotun Jihar Jigawa, wadda wani mai suna Alhaji Rabi’u Garba Aliyu ya kai a kan Cif Jude Okeke da wasu mutum uku. Cif Edozie Njoku ba ya cikin waɗanda ake ƙara.
“Ɗaya daga cikin buƙatun da aka nema a wajen kotu shi ne ‘A bayyana cewa shugabannin jam’iyyar All Progressives Grand Alliance na ƙasa, ciki har da mai ƙarar, waɗanda aka zaɓo su a babban taron ta na ƙasa da aka yi a Owerri, Jihar Imo, a ranar 31 ga Mayu 2019, su ci gaba da riƙe muƙaman su tare da yin ayyukan su har tsawon wa’adin shekara huɗu da za a lissafa daga ranar 31 ga Mayu 2021’.
“A ranar 30 ga Yuni 2021, Babbar Kotun Jihar Jigawa, a ƙara mai Lamba: JDU/022/2021 ta yanke hukunci inda ta ba wannan Alhaji Rabi’u Garba Aliyu nasara. Da aka ɗaukaka ƙarar, sai Kotun Ɗaukaka Ƙara ta bayyana cewa ƙarar da aka kai ba a bi dokar yin shari’a ba. Don haka, dukkan shari’ar da aka yi a Babbar Kotun Jihar Jigawa a ƙara mai Lamba JDU/022/2021, wadda Musa Ubale J ya yanke a ranar 30 ga Yuni 2021 da hukuncin da aka yanke mata duk an hamɓarar da su.”
Kotun Ƙoli, a hukuncin da ta yanke a ranar 14 ga Oktoba 2021, ta tabbatar da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta zartar.
“Sai dai kuma, a ranar 27 ga Janairu 2023, Cif Edozie Njoku, wanda bai taɓa zama cikin dukkan waɗancan shari’u da aka yi a kotuna daban-daban ba, ya je Kotun Ƙoli ta Nijeriya a matsayin wani wanda ke da ta cewa, ya shigar da buƙatar kotun ta yi gyara a ‘kuskuren rubutu da tuntuɓen alƙalami’ a ainihin babban hukuncin da Kotun Ƙolin ta zartar. An amince masa da hakan, kuma gyaran da aka yi bai shafi gundarin ƙarar da kuma hukuncin da Kotun Ƙolin ta riga ta yanke ba.”
A cewar Okoye, Hukumar Zaɓe hukuma ce mai bin doka da oda kuma za ta ci gaba da bin duk wata doka ko wani hukunci ko umarni da kotuna daban-daban su ka bayar a duk faɗin Nijeriya.
Ya ce, “Ba a ƙin bin umarnin kotunan idan sun ba da umarni ko su ka yanke hukunci ko wata shawara. Kuma su na da ƙarfin hukunta duk wanda ya yi masu tsaurin ido ya ƙi bin umarnin su da hukuncin su a tsarin da su ke da shi. Wannan shi ne abin da duk wani ɗan ƙasa ko wata ƙungiya da ya ke bin doka ya sani, maimakon ya koma ya na neman cin zarafi ko tursasawa ta hanyar wasu ƙungiyoyi marasa alƙibla don kawai a ɓata sunan hukumar da jami’an ta.”