A yau ne, wasu shugabannin kasashen duniya suka mika sakwanni don taya Xi Jinping murnar ci gaba da zama shugaban kasar Sin, bayan da aka sanar da cewa, an zabe shi a matsayin shugaban kasar a gun taron farko na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14.
A cikin sakon, shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha ya bayyana cewa, yadda taron majalisar wakilan jama’ar kasar Sin wato NPC ya zartas da wannan kuduri, ya shaida cewa, shugaba Xi Jinping yana da mutunci mai girma, kuma manufofin da ya tsara game da sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar Sin da kuma tabbatar da moriyar kasar Sin a dandalin duniya, sun samu goyon baya daga jama’ar kasar.
A cewarsa, kasar Rasha na yaba masa domin ya samar da gudummawa wajen raya dangantakar abota da taimakawa juna bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, tsakanin Rasha da Sin. Putin kara da cewa, ya yi imanin cewa, bisa kokarin da kasashen biyu suke yi tare, za a ci gaba da samun nasarori a fannoni daban daban a tsakaninsu. Kana zai ci gaba da yin mu’amala da shugaba Xi Jinping kan manyan batutuwan kasa da kasa da yankuna.
Har ila yau, a yau din, babban sakataren jam’iyyar kwadago ta kasar Koriya ta Arewa kuma shugaban kwamitin harkokin kasar Kim Jong Un, da babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar Lao People’s Revolutionary kuma shugaban kasar Laos, Thongloun Sisoulith, da shugaban kasar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange Touadéra, da shugaban kasar Comoros Azali Assoumanida, da shugaban kasar Italiya Sergio Mattarella, da kuma shugaban kasar Argentina Alberto Fernández, sun taya Xi Jinping murnar ci gaba da kasancewa shugaban kasar Sin. (Zainab)