Wani direban babbar mota da ya tsere bayan haddasa hatsari tare da kashe wata daliba mai suna Faith Aluku Adeshola, da ke karatun Difiloma a sashen Karatun aikin Jarida na Kwalejin Fasaha da ke Bauchi (Federal Polytechnic Bauchi).
Direban babbar motar ya buge marigayiya Adeshola, ne yayin da take ƙoƙarin ketare titi zuwa makaranta domin halartar darasin yamma.
- Sin Ta Ayyana Matakan Bunkasa Harkokin Sayayya Da Zuba Jarin Waje
- Bindigogi 3,907 Sun Yi Ɓatan-dabo A Hannun Rundunar ‘Yansandan Nijeriya – Majalisar Dattawa
Bisa bayanan da jarida LEADERSHIP ta samu, a lokacin da hatsarin ya faru, Faith tana kan babur a hanyarta ta zuwa makaranta, inda babbar motar ta buge su, wanda ya yi sanadin mutuwarta nan take, amma an kama direban motar da kuma mai babur din, kuma suna hannun ‘yansanda a halin yanzu.
Shugaban kungiyar dalibai ta makarantar (SUG), Comrade Haruna Umar, ya bayyana cewa marigayiya tana cikin shirye-shiryen kammala rajistar ta a makaranta ne ma kafin rasuwarta, kana ya roƙi ɗalibai da su kasance cikin hakuri da lumana, yana mai tabbatar da cewa hukumar makaranta da ta tsaro suna iya ƙoƙarinsu na ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da an yi adalci a kan lamarin.
Har ila yau, ya yi kira ga hukumar makarantar da ma Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC), da su girke tudu-tudu na rage gudu a kusa da makarantar domin kaucewa irin hatsarin nan gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp