Wata Hajiya mai shekaru 75 daga jihar Edo mai suna Adizatu Dazumi ta rasu a kasar Saudiyya bayan wata ‘yar gajeriyar rashin lafiya da ta yi fama da ita a lokacin da take aikin hajjin shekarar 2025.
Dazumi wacce ‘yar asalin Jattu Uzairue ce a karamar hukumar Etsako ta Yamma ta jihar Edo, ta rasu ne a ranar Litinin a babban Asibitin Sarki Fahad da ke birnin Makkah.
- ‘Yansanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Kisan Wata Matar Aure, ‘Yar shekara 22 A Kano
- Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Taron Kasa Na Yara Jagorori Na Kasar Sin
Shugaban tawagar Jin Dadin Alhazai, Musah Uduimoh ne ya sanar da rasuwar a ranar Talata.
Ya ce, mahajjaciyar ta kamu da rashin lafiya ne jim kadan bayan kammala Tawafi – zagaye dakin Ka’aba, inda daga nan aka kai ta asibiti a ranar Lahadi, a ranar Litinin kuma Allah ya yi mata cikawa.
“Kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, an yi jana’izar ta a Makkah a wannan rana, kuma an sanar da danginta a Jattu Uzairue a hukumance,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp