Wata babbar kotun tarayya a Abuja, ta yi watsi da karar da wasu mata masu zaman kansu, su shigar a gabanta, na ba su damar ci gaba da gudanar da karuwancinsu, ba tare da wata barazana ko tsangwama daga hukumomin tsaron gwamnatin tarayya ba.
Mai shari’a James Omotosho ne, ya yanke hukuncin a ranar Larabar, inda ya bayyana cewa; karuwai ba su da wani hakki na doka a duk wata doka da aka sani ko kuma kundin tsarin mulkin Nijeriya.
- Majalisar Dokokin Nijeriya Ta Zama Ƴar Amshin Shata — Kwankwaso
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban Miyetti Allah A Filato
Mai shari’a Omotosho ya bayyana cewa, za a iya kama karuwai a duk inda suke a gurfanar da su a gaban Kuliya, sannan za su iya fuskantar dauri na shekaru biyu a gidan yari, karkashin dokar laifuka da aka fi sani da ‘Penal Code’ a turance.
Karuwan, sun nemi kotu da ta hana Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja Nyesom Wike, da Hukumar Kare Muhalli ta Abuja, barazana, muzgunawa, kamawa da kuma gurfanar da su gaban shari’a a Abuja.
Sun kuma bukaci kotun da ta aiwatar da muhimman hakkokinsu na Dan’adam, wanda ya ba su damar yin karuwanci; kamar yadda suke sa ran suna da shi a tsarin dokokin Nijeriya.
Sai dai, a yayin da yake yanke hukuncin; mai shari’a Omotosho, ya yanke hukuncin cewa, ya yi watsi da karar tasu da suka shigar saboda rashin cancanta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp