Wuta ta kone wata tankar mai ɗauke da lita 33,000 na fetur, lamarin ya rutsa da wata mota kirar Toyota Prado Jeep da wata mota a unguwar Celica Junction, kan babbar hanyar Ife-Ibadan Expressway, a birnin Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Manajan da ke kula da sashen ayyuka a Hukumar Kashe Gobara ta Jihar, Akinyemi Akinyinka, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an sanar da su da misalin ƙarfe 6:27 na yamma ta wayar salula a ranar Alhamis.
Akinyinka ya ce tawagar jami’an kashe gobara ƙarƙashin jagorancin ACFS Adeniyi Adesina sun garzaya wurin lokacin da abin ya faru.
Da suka isa wurin, sun tarar da tankar mai cike da fetur da wata mota na ci da wuta.
Ya ce ma’aikatan kashe gobara sun fara aiki cikin gaggawa ta hanyar amfani da kumfar kashe gobara, kuma sun hana wutar bazuwa zuwa tashar mai ta NNPC da daƙile ɓarnatar da dukiyoyin da ke kusa da wurin da abin ya afku.
Ya ƙara da cewa, an haɗa kai da jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya wajen kashe wutar gaba ɗaya.
Akinyinka ya bayyana cewa gobarar ta samo asali ne daga matsalar birkin tankar yayin tafiya, lamarin da ya sa ta bugi mota kirar Toyota Prado da wata mota kafin ta faɗi a hanya inda nan-take ta wuta.
“Ba a samu asarar rai ba, amma tankar da mota ɗaya sun kone, yayin da Jeep ɗin ta faɗa cikin wani rami a sakamakon bugun da tankar ta yi mata. Hukumar kashe gobara ta ceci tashar mai ta NNPC da sauran kadarorin da ke kusa daga konewa,” cewar shi.
Mai ba da shawara kan ayyukan kashe gobara kuma shugaban kwamitin, Dr Maroof Akinwande, ya shawarci jama’a da su ci gaba da harkokinsu cikin kwanciyar hankali domin an kashe gobarar gaba ɗaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp