Duba da irin namijin kokarin da Shugaban Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, Dakta Abubakar Dantsoho, ke yi na shugabantar Hukumar Mujallar ‘The Reporters Nigeria Magazine’, ta zabe a matsayin gwarzonta na shekarar 2025, tare da karrama shi, da babbar lambar yabo.
A cewar mahukuntan Mujallar Dantsoho, ya sama gawarzonta na shekarar ne, musamman duba da gudunmawar da yake ci gaba da bayarwa, wajen inganta ayyukan Hukumar, wanzar da kasuwanci da kuma kokarin kai Hukumar zuwa matki irin ta duniya.
- An Bude Cibiyar Tattarawa Da Yada Labarai Ta Taruka Biyu Na Sin
- Gwamnatin Kano Za Ta Ɗau Nauyin Ɗalibai 1,002 Domin Karatu A Ƙasashen Waje
“A karsahin Shuagancin Dantsoho, Hukumar NPA ya ci gaba da inganta ayyukan Hukumar, inda hakan ya taimaka, ya kara habaka hada-hadar kasuwancin ketare na Hukumar na samar da Nijeriya Naira tiriliyan 5.81 kwatankwacin Dala biliyan 3.7, a zango na uku a 2024. ” Inji mahukuntan Mujallar.
A cewar mahukutan, daya daga cikin manyan nasarorin da Dantsoho ya samar shugabancin Hukumar shi ne, wanzar da dabarun Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, na rage yawan kudaden da kasar nan ke kashewa, wajen shigo da Mai daga ketare, ta hanyar yin amfani da Naira, wanda hakan ya rage yawan bukatar kudaden musaya na ketare.
Kazalika, mahukuntan Mujallar sun bayyana cewa, Dantsoho shi daya tilo, ya jagoranci zamowar Nijeriya, zama mamba a Kungiyar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta Kasa da Kasa wato IPCSA, musamman domin a tabbatar da ana bin ka’ida, a hada-hadar kasuwanci wato NSW.
“A karkashin Shugabancin Dantsoho, ya taimaka wajen ganin ana sauke sundukan kayan da aka yo jigilarsu a cikin sauki, musamman a Tashar Lekki wanda hakan ya taimaka, wajen rage cunkso a Tashar.” A cewar Mahukuntan Mullar.
Mahukuntan Mullar sun kara da cewa, sun zabo Dantso ne, ganin cewa, shi ne, na farko da aka zaba a mukamin Shugaba na Kungiyar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Gabas da yankin Afirka ta Tsakiya PMAWCA, inda zabarsa, ta kara daga kima da darajar Nijeriya, a fannin harkokin tafiyar da Tashohin Jiragen Ruwa, a yankin.
A yayin da yake karbar babbar lambar yabon Mullar Dakta Dantsoho ya bayar da tabbacin cewa, zai kara zage damtse wajen shugabantar Hukumar, daidai da tsare-tsaren Miniatan bunkasa tattalin arzki na Teku Adegboyega Oyetola, musaman domin Hukumar ta kara dorawa, kan nasarorin da ta zamar, ya zuwa yanzu.
Dantso ya kuma bai wa masu ruwa da tsaki a Hukumar ta NPA, tabbacin ci gaba da zuba duk wata kwarewa da yake da ita, domin a kara habaka tattalin arzikin kasar.
Ya sanar da cewa, lambar yabon, za ta karawa Hukumar karsashi wajen kara jajirewa na kara samar da damar hada-hadar kasuwanci, a daukacin Tashoshin Jiragen Ruwa na kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp