Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya bai wa shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, shaidar girmamawa na zama dan kasa a Abuja.
Wike ya karrama shugaban Senegal ne lokacin da ya tarbe sa a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a madadin shugaba Bola Tinubu a ranar Alhamis.
- Ƙananan Hukumomin Kano 14 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwan Sama — NiMET
- Noman Daminar Bana: Kisan Manoma Na Mayar Da Hannun Agogo Baya
Ministan ya ce, shaidar za ta bai wa shugaban kasar Senegal dukkan hakkoki da ‘yanci na dan kasa a babban birnin tarayya Abuja.
Har wa yau, za ta kasance wata alamar girmamawa da karfafa abota da kyakkyawar alakar da ke tsakanin Nijeriya da Senegal.
LEADERSHIP ta ruwaito, shugaba Faye na Senegal ya iso Nijeriya ne a ranar Alhamis, domin ganawa da shugaba Tinubu, wanda shi ne shugaban kungiyar raya arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS).