Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Nyesom Wike, ya gargaɗi jam’iyyar PDP da ka da ta kuskura ta miƙa tikitin takarar shugaban ƙasa ga wani ɗan Arewa a zaɓen shekarar 2027.
Wike ya faɗi haka ne a lokacin wata ganawa da ya yi da manema labarai a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa jam’iyyar na yi wa tsarin adalci da daidaito barazana idan har ta sake yin kuskuren da ta yi a 2023.
- Yanzu-yanzu: Matatar Ɗangote Ta Sake Karya Farashin Man Fetur
- Kaico: Wani Ƙani Ya Kashe Saurayin Yayarsa A Kano
“Me zai hana PDP ta ce tun da gaskiya ake nema, ɗan takarar shugaban ƙasa na 2027 zai fito daga kudu? Amma sun fi son sake yin wayo irin na bara, wanda ya sa jam’iyyar ta fuskanci rikici kuma ta sha kaye,” in ji Wike.
Wike ya ce yana da muhimmanci jam’iyyar ta bayyana matsayinta a fili tun kafin lokaci ya ƙure, domin hakan zai taimaka wajen sake gina amincewa da haɗin kai a tsakanin mambobin jam’iyyar.
Ya ƙara da cewa, “Idan shugaban ƙasa daga Kudu ya samu nasara a 2027, to a 2031 zai zama dama ce ga Arewa.
“Amma idan yanzu aka sake bai wa Arewa takara, wannan tsari tsakanin Arewa da Kudu zai ruguje.”
Wike, wanda tsohon gwamnan Jihar Ribas ne, yana daga cikin fitattun jiga-jigan PDP da ke goyon bayan daidaito da karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.
A baya dai, rikici wajen tantance daga inda ɗan takarar PDP zai fito ya janyo rabuwar kai a cikin jam’iyyar, lamarin da ya taimaka wajen rage ƙarfinta a zaɓen 2023.
Masana siyasa na ganin wannan gargaɗi na Wike na iya sake haifar da muhawara a jam’iyyar, musamman yayin da ta ke shirin fuskantar babban zaɓen 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp