Ministan Babban Birnin Tarayyar (FCT),Nyesom Wike ya jinjinawa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan bunkasa lamarin ilimi mai zurfi a fadin tarayyar Nijeriya.
Wike yace tsarin na Shugaban ya taimakawa bunkasar ilimin Jami’oi saboda taimakon da yake badawa na ilimin manyan makarantu.
- Za A Fara Amsar Bayanan Ɗalibai Masu Neman Lamunin Karatu A Ranar 24 Ga Watan Mayu – NELFUND
- Wike Ya Kwace Filaye 4,794 A Abuja Saboda Rashin Biyan Kudin Ka’ida
da yake jawabin lokacin da aka yi bikin gina Jami’ar na 50 da kuma yaye dalibai na 37,na Jami’ar Calabar, inda aka ba shi digirin girmamawa na digirgir na sashen shari’a, Ministan ya bayyna nau’oin taimakawa ilimi kamar su kafa hukumar ba dalibai rance kan neman ilimi wanda ake bawa dalibai saboda kara ilimi mai zurfi (NELFUNd).
Ya ce ta hanyar bada bashin karatu ga daibai hakan ya taimaka da kuma tabbatar da cewar rashin kudi bai hana hanyar samun ilimi mai nagarta ba.
A sanarwar da take dauke da a hannun mai ba shi shawara na musamman ma kan hulda da jama’a da kuma kafofin sadarwa na zamani, Lere Olayinka, Wike ya bayyana gudunmawar da Shugaban kasa ya bada,da suka hada da yadda dalibi zai fara yin abinda ko/abubuwan,da za su sa ya zamana mai dogaro da kansa,wani tsari ne da aka vullo da shi musamman saboda matasa wadanda za su yi amfani da ilimin da suke da shi wajen gabatar da harkokin kasuwanci.
Ya kara da cewa cire Jami’oi daga tsarin albashi na (IPPIS),wanda hakan ne ya ba su Jami’oin tsayawa da kansu kan lamarin da ya shafi ayyukansu wanda har ila yau hakan ya sa ayyukamsu suka kara ingantuwa.
Wike ya yi karin bayani,“akwai maganar amincewa da maganar kudaden bincike na Hukumar TETFund a cikin wasu makarantu, hakan ya kar bunkasa lamarin daya shafi bincike da kirkiro wasu abubuwa.”
Su wadannan lamurran na ci gaba sun kara daidaita Jami’oi su maida hankali kan ilimin da suke samarwa domin ya cimma matsalolin da ake fuskanta a karni na ashirin da daya.
da yake bayyana yadda ya ji dangane da karramawar da Hukumar Jami’ar kalaba ta yi masa na ba shi digirin digirgir,Wike ya ce ita karramawar wata girmamawa ce har ila yau,da kuma jan hankalinsa na ya ci gaba da yin ayyukan raya kasa,domin ya jawo hankalin matasa wadanda ke tasowa.
“da na amince da wannan karramawar ina mai farinciki wannan haka nake jin da annashuwa har cikin zuciyata domin zan ci gaba da bayar da gudunmawa sosai kan harkar data shafi ilimi, tafiyar da gwamnati kamar yadda ya dace da kuma ci gaban kasa.
“Ina mai matukar farincikin domin kuwa lamarin ya shiga zuciyata sosai,Jami’ar kalaba ta sa sunana ya cikin tarihin da ake ajiya da zinari,shi yasa ina mai kara yi maku godiya kamar yadda ya jaddada,”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp