Hukumar dake sa ido kan ikon mallakar fasaha ta kasa da kasa wato WIPO, ta gabatar da rahoton ma’aunin kirkire-kirkire na duniya na shekarar 2024 a jiya Laraba, a bikin makon ikon mallakar fasaha na 2024 da aka gudanar a Singapore.
Rahoton na nuna cewa, Sin ta mallaki rukunonin kamfanoni 26 masu kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha dake cikin matsayin 100 dake kan gaba a duniya, kuma wannan adadi ya kai 24 a bara, inda Amurka ke biye da ita bisa mallakar guda 20. Wannan adadi ya kai 8 a Jamus, kuma Indiya da Koriya ta kudu kowanensu na da guda 4.
Kazalika, rahoton ya ce, cikin wurare mafiya karfin kirkire-kirkire dake matsayin 10 na farko a duniya, 7 daga cikinsu suna Asiya, 3 kuma suna Amurka. Wato Tokyo-Yokohama na Japan yana matsayin farko, sai Shenzhen-Hongkong-Guangzhou dake kasar Sin, Beijing kuma ya daga matsayinsa zuwa na 3, San Jose na California – San Francisco yana matsayi na 6, wanda ya kasance rukuni mafi karfin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha a Amurka. (Amina Xu)